ZUWA GA 'YAN UWA MATA
Aure shine mafi girman al'amari arayuwar 'Ya mace. Ta hanyarsa ne zata samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta samu damar kafa nata iyalin.
Idan aure yayi jinkiri agareki, kar kiyi amfani da wannan damar wajen biyan bukatar sha'awarki ta hanyoyin da Ubangijinki ya haramta.. A'a kiyi hakuri ki kama kanki. Ki dage wajen ibadah da neman yardar Ubangijinki.
Ki kyautata zato ga Ubangijinki. Shi mabuwayi ne mai hikima. Kuma duk abinda ya Qaddara miki, to kiyi fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi sannan ki nemi mafita awajensa, ba wajen bokaye da 'yan bori da 'Yan duba ba..
Zina da Ma'digo da kallon hotunan batsa, da yin chatting na batsa duk Kofofin samun tsinuwa ne da kuma fushin Ubangijinki.. Ki kyautata ma kanki kiji tsoron Ubangijin da ya halicceki kar ki kai kanki ga Hallaka.
Ki kiyayi hulda da mayaudaran samari wadanda ke kanki kin san ba aure ne yake kawosu wajenki ba. Mafiya yawansu zasu bata miki lokaci ne kawai. Idan kuma lokacin aurensu yayi suje su auri wata daban bake ba.
Ki kiyayi saurayin da zai rika yabon surar jikinki, ko kuma ya rika yi miki wasu kalaman da bai kamata arika jinsu awajen mutum mai kunya ba. Mafiya yawansu sha'awarsu ce ta kawosu gareki ba wai soyayyar gaskiya ba. Idan ya kawar miki da budurci ya lalata rayuwarki shikenan tafiyarsa zai yi.
Ki kori duk saurayin da kika ga alamar dan iska ne, wanda idan kuna hira yana yunkurin ta'ba sassan jikinki, Koda ya riga ya biya sadakinki kar ki yarda ya jefaki a layin mazinata ta hanyar ta'ba jikinki, ko kuma Zina. Duk mai kaunarki domin Allah ba zaiso ya janyo miki azabar Allah ba.
Idan kika aikata wani abu daga cikin wadannan, to kinci amanar kanki, Kin ci amanar Iyayenki, Kinci amanar dukkan 'yan uwanki da danginki, kinci amanar 'Ya'yan da zaki haifa nan gaba.... Sannan Uwa-Uba kinci amanar ALLAH DA MANZONSA (SAWW).
WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU, Mun rubuta ne domin isar da Sakon Allah da Manzonsa izuwa zukatan masu rabo. Allah yasa damu daku mu samu tsira aduniya da lahira. Allah shi kiyayemu daga ZINA da dukkan dangoginta. Aaameeen.
ZAUREN FIQHU (07064213990) zaku iya tuntubarmu ta email domin tambayoyi, magunguna ko shawarwari (zaurenfiqhu@gmail.com)
Comments
Post a Comment