MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 12

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata ga Annabinmu tare da iylan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyan bayansu da kyutatawa.

Wannan shine ci gaban darasinmu na Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke kawo muhimman lamura acikin tarihin Ma'aikinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

ZAMANSA A KOGON HIRA'U
*****************************
Annabi (saww) ya kasance akowacce shekara yakan kebance kansa tsawon wata guda ya tafi kogon hira'u wanda ke kan Jabalun Nur ya zauna yana tunani cikin lamarin Ubangijinsa kuma yana ibadah (bautar Allah) bisa addinin Kakansa Annabi Ibrahim (alaihis salam).

Wannan tun kafin ya cika shekaru arba'in aduniya kenan. Amma bayan ya cika 'dan shekara arba'in aduniya watarana yana zaune acikin kogon sai ya hangi siffar wata Halitta mai girman gaske ta cika dukkan sasanni. Ashe Shugaban Mala'iku ne wato Jibreelu (amincin Allah ya tabbata gareshi).

Yazo ya rungumeshi zuwa jikinsa runguma mai tsanani sannan ya sakeshi, yace masa "YI KARATU".

Sai Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace masa "NI BA MAI KARATU BANE".

Sai ya sake rungumarsa da karfi, ya sakeshi ya sake ce masa "YI KARATU". Yace masa "NI BA MAI KARATU BANE".

Sai ya sake rungumarsa da karfi a karo na uku, ya sake sakinsa yace masa "YI KARATU". Yace masa "NI BA MAI KARATU BANE".

Sai Jibrilun yace "YI KARATU DA SUNAN UBANGIJINKA WANDA YAYI HALITTA.

"YA HALICCI MUTUM DAGA GUDAN JINI".

"YI KARATU DOMIN UBANGIJINKA SHINE MAFI KARAMCI".

"SHINE WANDA YA SANAR TA HANYAR ALQALAMI"

"YA SANAR DA MUTUM ABINDA BAI SANI BA". (Suratul 'Alaq ayah ta farko zuwa ta biyar).

Daga nan sai ya sakeshi yana ce masa "YA MUHAMMADU!! HAKIKA KAI MANZON ALLAH NE!!!".

Nan take sai Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam)  ya koma gida wajen Maidakinsa (Nana Khadijah) alhali zazzabi mai zafi ya rufeshi kasancewar wannan shine karon farko da ya ta'ba ganin Mala'ika ido da ido awannan duniyar.

Da yaje gida ya bata labarin dukkan abinda ya faru dashi, ita kuma taci gaba da kwantar masa da hankali tare da kalamai masu dadi. Tana ce masa "Ya Muhammadu wallahi har abada Allah ba zai ta'bar dakai ba. Domin hakika kai kana sadar da zumunta, kana ba ma marar abun hannu, Kuma kana taimako bisa matsalolin zamani".

Wadannan ayoyin guda biyar da Mala'ikan ya gaya masa sune farkon wahayin da ya sauka na Alqur'ani.

Salati da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu da iyalan gidansa sau adadin yadda masu ambato suka ambaceshi, da kuma adadin yadda rafkananni suka rafkana daga barin ambatonsa. Albarkacin wannan salatin Ya Allah ka Qara raya harsunanmu da zukatanmu cikin ambatonka da yawaita salati gareshi ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 3. AN GABATAR DA KARATUN ARANAR (23/12/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI