DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA KUNSA (KASHI NA 2)
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban Mutane da Aljanu, Limamin Mala'ikun Allah, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa Shiryayyu. Idan Daliban ZAUREN FIQHU basu manta ba, Wannan shine darasi na biyu acikin karatunmu mai taken DUNIYAR ALJANU DA SHAITANU. Kuma in sha Allahu zamu dora ne daga wajen da muka tsaya. Duk da cewa mukan gutsuro wani abu daga cikin wannan darasin kusan kullum. Maudhu'in da zamu tattauna akansa ayau shine: SHIN ALJANU SUNA CIN ABINCI KUWA? Akwai sabanin Malamai akan wannan mas'alar bisa Qauli guda uku kamar haka: Daga cikin Malamai akwai wadanda suke ganin cewa Aljanu basu cin abinci kwata kwata. Sun kafa hujjah da cewa ai tunda su Aljanu da shaitanu basu da jiki irin na Bil Adama, Wato jikinsu kamar iska ne. Don haka basu da bukatar cin abinci. Gaskiya wancan zance ne marar Hujjah. Don haka ba zai zama karbabbe ba. Akwai kuma Malamai wadanda suke ganin