DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA KUNSA (KASHI NA 2)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban Mutane da Aljanu, Limamin Mala'ikun Allah, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa Shiryayyu.

Idan Daliban ZAUREN FIQHU basu manta ba, Wannan shine darasi na biyu acikin karatunmu mai taken DUNIYAR ALJANU DA SHAITANU. Kuma in sha Allahu zamu dora ne daga wajen da muka tsaya. Duk da cewa mukan gutsuro wani abu daga cikin wannan darasin kusan kullum.

Maudhu'in da zamu tattauna akansa ayau shine:

SHIN ALJANU SUNA CIN ABINCI KUWA?

Akwai sabanin Malamai akan wannan mas'alar bisa Qauli guda uku kamar haka:

Daga cikin Malamai akwai wadanda suke ganin cewa Aljanu basu cin abinci kwata kwata. Sun kafa hujjah da cewa ai tunda su Aljanu da shaitanu basu da jiki irin na Bil Adama, Wato jikinsu kamar iska ne. Don haka basu da bukatar cin abinci. Gaskiya wancan zance ne marar Hujjah. Don haka ba zai zama karbabbe ba.

Akwai kuma Malamai wadanda suke ganin cewa Aljanun sun kasu zuwa gida biyu ne: Wato akwai wasu daga cikin Nau'in shaitanu da Aljanu wadanda sukan ci abinci. Akwai kuma wadanda basu ci.

Wadannan sun dogara ne da hadisin nan wanda Ibnu Abdil-Barri ya ruwaito daga Wahbu bn Munabbih (rah) yana cewa:

"ALJANU KALA-KALA NE. TATATTUNSU ISKOKI NE. BASU CI BASU SHA, KUMA BASSU HAIHUWA. AKWAI KUMA WADANDA SUNA CI DA SHA, KUMA SUNA SHA. ACIKINSU NE AKE SAMUN SU F PATALWA, GWAIGWAI, KWARANGWAL, ETC.

- Hafiz Ibn Hajr Al-Asqalaniy ne ya kawo wadannan zantukan acikin FAT-HUL BAARIY juzu'i na 6, shafi na 345.

Kuma sun kafa hujjah da hadisin nan na Abu Tha'alabah Alkashaniy (ra) wands Manzon Allah (saww)  ya fadi nau'in yadda Aljanu suke.

Wadannan hujjojin nasu za'a iya dauka ayi aiki dashi.

Qauli na uku kuma Malaman suka ce: Dukkanin Aljanu suna ci suna sha.
Akwai hadisai Sahihai masu yawa wadanda suka fito fili Qarara da bayanin cewa Lallai Aljanu suna cin abinci kuma suna sha. To wannan zancen yafi Qarfi fiye da kowanne. Saboda hadisai masu zuwa kamar haka:

Misali akwai hadisi acikin Sahihul Bukhariy daga Abu Hurairah (ra) cewa ya kasance yana dauke da ruwa domin Alwalar Manzon Allah (saww). Sai Watarana Manzon Allah (saww) ya zaga domin biyan bukatarsa, Sai ya tambaya:

"SHIN WANENE WANNAN?" Nace "Abu Hurairah ne". Sai yace "KA TAHO MIN DA DUWATSU INYI 'DAHARA DASU. AMMA KAR KA KAWO MIN QASHI KO KASHIN DABBOBI".

Sai na taho masa da duwatsu ina dauke dasu acikin tufafina. Har sai da na ajiyesu agefensa. Sannan na juya. Har sai da ya kammala, Sai na tafi tare dashi. Sai nace masa :

"Menene laifin Qashi ko kashin dabbobi?". sai yace min "HAKIKA SU WADANNAN BIYUN SUNA DAGA CIKIN ABINCIN ALJANU NE. DOMIN HAKIKA JAMA'AR ALJANUN NASIBEENA SUNZO GARENI, MADALLA DA WADANNAN ALJANUN.

DA SUKA TAMBAYENI GUZURI SAI NA ROKI ALLAH CEWA KADA SU WUCE TA KUSA DA WANI QASHI KO KASHIN DABBOBI FACHE SAI SUN SAMU ABINCI AKANSA".

(Aduba Sahihul Bukhariy hadisi na 3,860).

To kunga kenan koda wannan hadisin ma kadai ya isa hujjah akan cewa Aljanu suna cin abinci. Bayan su dinma har shaitan ma yana cin abinci kuma yana sha.

Akwai hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:

"IDAN DAYANKU ZAI CI ABINCI, TO YACI DA HANNUNSA NA DAMA. KUMA IDAN DAYANKU ZAI SHA RUWA, TO YASHA DA HANNUN DAMANSA. DOMIN HAKIKA SHI SHAITAN YANA CIN ABINCI DA HANNUNSA NA HAGU NE, KUMA YANA SHA DA HANNUNSA NA HAGU NE".

(aduba Sahihu Muslim hadisi na 202).

Kaga wannan hadisin ya tabbatar mana da cewa Lallai shaitan yana ci yana sha. Don haka ma aka hana muyi koyi dashi awajen cinmu da shanmu.

Hakanan acikin Sahihu Muslim akwai wani hadisin daga Sayyiduna Huzaifah ibnul Yamaan (ra) yace:

"Mun kasance idan mun halarci wajen Cin abinci tare da Manzon Allah (saww) Bama tsoma hannayenmu har sai bayan Manzon Allah (saww) ya fara.

Rannan munzo cin abinci tare dashi (saww) sai ga wata Kuyanga. Ta taho kamar wacce aka korota aguje. Tazo zata sanya hannunta kenan acikin abincin Sai Manzon Allah (saww) ya rike hannun nata.

Sai Kuma ga wani Balaraben Qauye nan ya taho shima kamar wanda ake tunkudoshi. Yazo zai sanya hannu sai Manzon Allah (saww) ya rike hannun nasa. Sannan yace:

"HAKIKA SHI SHAITAN YANA SO YA FARA CIN ABINCIN NAN NE  BA TARE DA AN AMBACI SUNAN ALLAH BA.

HAKIKA SHINE YAZO DA WANNAN KUYANGAR DON YA HALASTA MA KANSA ABINCIN SAI NA RIKE HANNUNTA, SAI KUMA YAZO DA WANNAN BALARABEN QAUYEN DON YA HALASTA MA KANSA ABINCI. SHIMA NA RIKE HANNUNSA. NA RANTSE DA WANDA NUMFASHINA KE HANNUNSA, HAKIKA HANNUNSA YANA CIKIN HANNUNA TARE DA NATA".

Daga nan sai Manzon Allah (saww) yayi basmalah ya fara cin abincin".

(Aduba Sahihu Muslim hadisi na 2017).

Kun ga wannan abinda ya faru a wannan hadisin ya Qara tabbatar mana da cewa Ba ma aljanu ba, Shi kansa shaitan dinma yana ci yana sha. Harma yakan shiga jikin wani domin yaci abincin ta jikinsa Mutukar dai ba'a yi Bismillah akan abincin ba.

Akwai wani hadisin hakanan acikin Sahihu Muslim daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace yaji Manzon Allah (saww) yana cewa:

"IDAN MUTUM ZAI SHIGA GIDANSA SAI YA AMBACI SUNAN ALLAH YAYIN SHIGARSA DA YAYIN CIN ABINCINSA, SAI SHAITAN YACE (WATO YA GAYA MA 'YAN UWANSA SHAITANU)  BAKU DA WAJEN KWANA ANAN KUMA BAKU DA ABINCI".

AMMA IDAN MUTUM YAZO SHIGA (GIDANSA) BAI AMBACI ALLAH BA, SAI SHAITAN YACE "KUN SAMU WAJEN KWANA".

IDAN KUMA BAI AMBACI ALLAH A YAYIN CIN ABINCINSA BA, SAI (SHAITAN YA GAYA MA 'YAN UWANSA SHAITANU) KUN SAMU WAJEN KWANA ANAN DA KUMA ABINCI".

(Sahihu Muslim hadisi na 2018).

Daga cikin fa'idodin da muka samu acikin acikin karatun nan na yau, akwai muhimmancin yin zikirin Allah alokacin shigowa gida da kuma lokacin cin abinci.

Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba in sha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1) 18 - 10 - 2015.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI