FALALAR FA'DAR LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI :
Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugaban Annabawa da Manzanni, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da Masu binsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Wannan bayani ne game da falalar "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM".
Kasancewar muna yawan bada shawarar arika yawaita yinta, acikin fatawoyinmu na Zauren Fiqhu, shi yasa naga zai yi kyau mu fa'di falalarta sosai yadda mutane zasu ji su Qaru, kuma su riketa sosai.
Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (Allah ya yarda dashi) yace "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi) yace mun "KACE LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH DOMIN HAKIKA ITA TASKA CE DAGA TASKOKIN ALJANNAH".
To kunga ashe kenan yawaita fa'darta zai iya zama dalilin samun waccen taskar ta lahira, tare da rahamar Allah. Sannan kuma ya wadata mutum tun daga nan duniya.
Mak'hul (rah) daya daga cikin magabata na kwarai yace "Duk wanda yace 'LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI WALA MANJAA MINAL LAHI ILLA ILAIHI' to Allah zai toshe masa kofofin abubuwan chutarwa har guda saba'in, mafi Qankantarsu ita ce talauci.
To ashe kenan duk wanda ke neman budi da yalwar arziki, ko samun ciniki mai albarka a kasuwancinsa, ko daukaka awajen aikin Gwamnati to ya yawaita fa'din wannan zikirin tare da gaskatawa azuciyarsa. In shaAllah zai samu biyan bukatarsa.
Acikin wata riwayar kuma aka ce "Duk wanda ya fa'di LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL LAHI, zata zamo masa maganin chututtuka chasa'in da tara. Mafi sauki daga cikinsu shine baqin ciki.
To ashe kenan duk wanda Makiya suka sashi gaba, ko baqin ciki ya dameshi, ko kuma wata chuta acikin jikinsa, ko larura irin ta jinnu, idan ya yawaita La haula in shaAllah zai samu lafiya.
Manzon Allah (saww) ya kasance yana cewa "KU YAWAITA DAGA SHUKE-SHUKEN ALJANNAH - (WATO) LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH".
Kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya kasance yana cewa "Duk wanda yayi wa ni'ima, Kuma yake bukatar ni'imar ta wanzu, to ya yawaita fa'din La haula wala Quwwata illa bilLah".
Wato idan Allah ya baka wata ni'ima ta duniya, kamar arzikin 'Ya'ya ko Mata ko dukiya ko abin hawa, ko daukaka atsakanin mutane, to idan ka yawaita La haula Allah zai kiyayeka daga sharrukan mahassada da makiya da kuma duk wani abinda zai janyo maka gushewarta.
Kuma Manzon Allah (saww) yace "Duk wanda maqiya suka kamashi, kuma bashi da mai Qwatarsa to ya rika fa'din La haula Wala Quwwata illa Bil Lah'.
Aufu bn Malik Al-Ashja'ee (rta) yace "Yayin da abokan gaba suka kamani, na yawaita fa'dinta sai sasarin da suka daureni dashi ya yanke ya zube qasa. Na fito daga garin nasu har na kore rakumansu na taho na shigo garinmu dasu".
Idan baku manta ba, anan Zauren Fiqhu munyi Qissar wannan Sahabin (Aufu bn Malik) wanda kafirai suka saceshi suka tafi dashi suka daureshi a daki, to yana ta fa'din La haula wala Quwwata illa Bil Lah din nan, har Allah yasa wannan sasarin ya kunce, kuma ya dawo gida tare da dabbobi masu yawa. Dashi da mahaifansa sun samu arziki da chanjin rayuwa ta dalilin wannan kalmar.
Anan nake bada shawara ga jama'a musamman wadanda suke zaune a yankunan da ake yawan kidnapping din mutane, cewa su yawaita yin wannan kalmar safiya da maraice domin samun kariyar Allah daga sharrin wadannan barayi. Wanda kuma Allah ya jarabceshi suka kamashi, to ya yawaita yinta har Allah ya fiddashi daga hannunsu.
Haka kuma akwai wata baiwar Allah wacce shaidanun Aljanu suka zo suka cika mata gidanta. Tana ganinsu Qarara sunce su dubu dari uku ne (300,000) gaba dayansu. Basu barinta ta zauna agidan. Don haka ta garzayo nan Zauren Fiqhu aka bata taimako.
Na bata shawarar ci gaba da yin La haula wala Quwwata illa Billahil Aliyyil Azeem. Ta rantse mun da Allah cewa duk lokacin da ta fa'di wannan kalmar sai taga wani abu kamar takobi yana yanyanka Shaidanun Aljanun, wani lokacin kuma taga wuta tana kamasu, da haka ta mafiya yawansu suka mutu, sauran kuma suka gudu daga gidan. Alhamdulillahi.
La haula wala Quwwata illa Bil Lah, maganin shaidanun Aljanu ce. Kuma tana dakile sharrinsu da waswasinsu ajikin Dan Adam. Haka kuma koda sihiri aka yiwa mutum, to ya yawaita wannan zikirin tare da ikhlasi. In shaAllah zai samu waraka da ikon Allah. Koda matan da suke bukatar samun mijin aure, su rika yawan yinta. In shaAllah Ubangiji zai bullo musu da masoyi na kirki wanda zasu aura.
Idan mijinki ne ya juya miki baya ba tare da laifinki ba, to ki yawaita wannan zikirin. In shaAllah Allah zai jefa soyayyarki acikin zuciyarsa kuma ya baki rinjaye akan masu shiga tsakaninku. In shaAllah. Amma ki kyautata niyyarki domin Allah yana kallon qudurin zukata.
Haka kuma masu Sana'a da masu neman aiki. Ko kuma wanda harkokinsa suka chushe. A yawaita fa'dar La haula wala Quwwata illa Bil Lah. Musamman a muhimman lokutan da Allah ke amsar addu'ar bayinsa. Misali kamar karshen dare, bayan sallolin farillah, etc.
Zauren Fiqhu ya rairayo wadannan bayanai ne daga littafin KASHFUL GUMMAH na Sayyidi AbdulWahhab Ash-Sha'araniy (rahmatullahi alaihi) acikin Mujalladi na daya, shafi na 349.
Anan zamu tsaya, da fatan Allah ya mafanar damu da abinda muka karanta.
An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp 3 ranar 1/07/1440 07/03/2019.
Comments
Post a Comment