MADUBIN DUBAWA (067)
Wani labarin abin tsoro ne wanda ya faru tun zamanin Tabi'ai, Zauren Fiqhu ya bincikoshi domin ya zama abin lura garemu acikin rayuwarmu. Gashi nan kamar haka :
Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Umar bn Harun daga AbdulHameed bn Mahmud Almu'awwaly, yace :
"Na kasance ina zaune awajen Abdullahi bn Abbas (Allah ya yarda dashi) sai ga wasu mutane sun zo wajensa suka gaya masa cewa :
"Mun fito ne zamu je aikin Hajji akwai wani abokinmu tare damu. Sai da muka iso wani waje da ake kira "Zatus Sifahi" sai Allah ya karbi ransa.
Mun gyarashi (wato munyi masa wanka mun sanya masa likkafani) mun je mun tona masa Qabari munyi masa lahdu (wato mun tona masa 'yar ciki din nan). Bayan mun kammala sai muka tarar da bakaken macizai sun cika Qabarin nasa fal!.
Yayin da muka tona masa wani Qabarin dabam sai muka sake tarar da wasu macizan acikinsa shima.. Sai muka sake tona masa wani Qabarin, amma shima muka ga macizan sun cikashi, shine muka kyaleshi muka taho gareka (neman fatawa).
Sai Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (Allah ya yarda dashi) yace "Wannan macizai da kuke gani, ai ayyukansa ne da ya kasance yana aikatawa. Kawai kuje ku binneshi acikin wani daga Qaburburan nan".
Bayan sun koma gida sai suka tambayi matarsa shin menene abokin nan namu yake aikatawa aboye har wannan mummunan abu ya sameshi haka?.
Sai tace "Shi ya kasance dan kasuwa ne yana sayar da kayan abinci har da irin su garin alkama haka, kullum acikinsa yake aunar abinda za'a ci agidansa, sannan ya samo dusa gwargwadon abinda ya auna, sai ya chakuda acikin wanda yake sayar ma jama'a (wato Algus yake yi acikin kasuwancinsa yana chutar da jama'a).
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
Zauren Fiqhu :
**************
Hakika wannan babban gargadi ne ga duk wanda yake cin amanar al'ummah ta hanyar ha'intarsu ko algus ko danne hakkokinsu, ko wawure dukiyarsu ko satar kudadensu ko kadarorinsu. Hakika mu dukkanmu daga Allah muke kuma gareshi zamu koma babu makawa!! Kuma zai yiwa kowannenmu sakayyar abinda ya kasance yana aikatawa.. (Na alkhairi ko sharri).
Kada dadin duniya ya rudeka ka rika jin tamkar ba zaka koma ga Allah ba!! Kar kaga kamar Allah ya barka kana aikata sa'bonsa bai kamaka ba, A'a ranar damqarka tana nan tafe. Kuma wannan jinkirin da yayi maka tamkar gadar zare ce.. Ubangijinka yana nan a madatsa kuma zakaje ka tarar dashi..
Ya Allah kayi mana rangwame ka yafe mana miyagun ayyukanmu, ka karbi tubanmu don falalarka da rahamarka ka gafarta mana ka gyara ayyukanmu ka lullubemu da bargon rahamarka. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU +2347064213990 (01/03/2019 24/06/1440).
KU TURA MA 'YAN UWA MUSULMAI DOMIN HAKIKA MUTUWA WA'AZI CE..
Comments
Post a Comment