GORON JUMA'AH (20/11/2020)
Zuwa ga 'Yan uwa Musulmai masu yin rubuce-rubuce akan Social Media, da masu yin magana ko wa'azi a masallatai dal kafofin watsa labarai, musamman Malamai da 'yan siyasa. Ya zama wajibi duk sanda zamuyi magana akan wani mutum ko wasu mutane mu rika yin adalci tare da lura da wasu abubuwa kamar haka : - Kar ka manta cewar shima musulmi ne, kuma baka da tabbacin cewar kai kafishi matsayi agun Allah. - Ka rika tuna cewar Manzon Allah (saww) yace : "Duk wanda yake bibiyar laifin wani musulmi, shima sai Allah ya bibiyi laifukansa, kuma duk wanda Allah ya bibiyi laifukansa to sai ya kunyatar dashi koda atsakar gidansa ne". - Kar ka manta cewar idan kayi masa karya ko Qage, tofa bazaka mutu ba, har sai Allah ya jarrabeka ka aikata irin laifin da kake tuhumarsa akai. - Kar ka manta cewar duk lokacin daka shagaltu da kallon laifukan mutane don yin tonon silili garesu, kai kuma sai Allah ya bayyanar da boyayyun laifukanka, wani lokacin ma har duk wani abin kunyar da iyaye