GORON JUMA'AH (20/11/2020)

Zuwa ga 'Yan uwa Musulmai masu yin rubuce-rubuce akan Social Media, da masu yin magana ko wa'azi a masallatai dal kafofin watsa labarai, musamman Malamai da 'yan siyasa. 

Ya zama wajibi duk sanda zamuyi magana akan wani mutum ko wasu mutane mu rika yin adalci tare da lura da wasu abubuwa kamar haka :

- Kar ka manta cewar shima musulmi ne, kuma baka da tabbacin cewar kai kafishi matsayi agun Allah. 

- Ka rika tuna cewar Manzon Allah (saww) yace : "Duk wanda yake bibiyar laifin wani musulmi, shima sai Allah ya bibiyi laifukansa, kuma duk wanda Allah ya bibiyi laifukansa to sai ya kunyatar dashi koda atsakar gidansa ne".

- Kar ka manta cewar idan kayi masa karya ko Qage, tofa bazaka mutu ba, har sai Allah ya jarrabeka ka aikata irin laifin da kake tuhumarsa akai. 

- Kar ka manta cewar duk lokacin daka shagaltu da kallon laifukan mutane don yin tonon silili garesu, kai kuma sai Allah ya bayyanar da boyayyun laifukanka, wani lokacin ma har duk wani abin kunyar da iyayenka ko danginka suka aikata sai ya fito fili Qarara kowa ya sani. 

- Kada kaqi musulmi saboda bambancin siyasa. Domin hakika watarana sai kayi nadamar zagin da kayi masa tun anan duniya. Aranar lahira kuma ladanka za'a kwashe a biyashi alhakin zagi ko cin mutuncin da kayi masa. 

- Kada kaqi mutum saboda bambancin dariqah ko kungiyar da yakeyi. Domin hakika aranar Alkiyamah Allah bai yi alkawarin zai kyale wani mutum saboda sunan Qungiya ko dariqar da yakeyi ba. Kyakkyawan aiki da kyawun halaye sune gaba. 

- Ka kiyayi harshenka domin hakika mafiya yawan 'yan wuta harshe ne yake kaisu.

- Kar ka lalata lahirarka don gyaran duniyar wani.. Ko wanene. Kada ka zagi wasu mutane don mayar da martani ga wasu.. Ka kiyayi zagi ko yarfe akan mutumin da bakayi zamani dashi ba, kuma bai shiga hakkinka ba. Watakil shi ya fika matsayi agun Allah. 

Allah Madaukakin Sarki yace : "KADA KIYAYYAR WASU MUTANE YA HANAKU YIN ADALCI (GARESU) KUYI ADALCI SHINE MAFI KUSA DA TSORON ALLAH".

- Ka kiyayi zagin Malamai ko Shugabanni ko mutane masu mutunci. Rashin albarka yana iya samunka har karshen rayuwarka. 

Kuma Manzon Allah (saww) yace "AZABA TA TABBATA GA WANDA ZAI KIRKIRI LABARI DOMIN YA SANYA MUTANE DARIYA, AZABA TA TABBATA GARESHI, AZABA TA TABBATA GARESHI!!!".

Ranar Alkiyama rana ce wacce zaka maida bahasi akan kowacce maganar daka furta ko ka rubuta... Kafin ka rubuta abu ka rika tunanin wadancan abubuwan dake sama. 

Allah shi tabbatar damu bisa Sunnar Fiyayyen halittu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (20/11/2020 05/04/1442).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI