JINNIYYATUL ASHIQAH (ALJANAR SOYAYYA)

Ita wannan Aljanar kamar yadda muka sha yin bayani ashekarun baya anan Shafin Zauren Fiqhu, yanayin shafarta da kuma Muguntar da take yiwa 'Dan Adam kusan irin na JINNUL ASHIQ ne. Sai dai ita har ta zarce Jinnul Ashiq wajen Mugunta da cin zalin 'Dan Adam. 

JINNIYYATUL ASHIQAH Aljana ce Mace wacce takan shiga Jikin Mazajen Bil Adam bisa dalilin soyayya, (wato hujjarta wajen shuga jikinsu kenan wai sonsu takeyi). 

Irin wannan Aljanar ayawancin lokuta takan yi kokarin dulmiyar da 'Dan Adam din cikin hallaka da sa'bon Allah  ta hanyar chanza masa dabi'u daga Kyawawa zuwa munana.. Wani ma takan hanashi gudanar da ibadunsa kamar sallah ko Azumi ko karatun Alqur'ani da sauransu. 

Wani lokacin takan fara yin Zina da Mutum tun yana yaro Qarami. Wani ma zaka ga shekarunsa basu wuce biyar ko shida ba,  amma ahakan zata zo ta rika saduwa dashi.

Irin wadannan Shaitanun sukan dauke Mutum su tafi dashi acikin mafarki don biyan bukatar kansu. Misali akwai wani yaro wanda ita tashi takan daukeshi zuwa gefen wani Kogi ko Teku, takan yi kwana da kwanaki tana Zina dashi sannan ta dawo dashi. (Amma, shi wannan a zahiri yake ganinta). 

Wani kuma takan yi masa illoli ajikinsa misali ta chanza masa kamanninsa, ko ta snaya masa wata chuta acikon jikinsa wacce zaiyi ta fama da ita shekara da sgekaru, wani kuma takan 'daure masa al'aurarsa, Koda bayan ya girma sai al'aurarsa ta koma Qarama sosai kamar ta Qananan yara. 

Akwai kuma wanda Aljanar takan cire masa son aure daga Zuciyarsa. Zai zamanto ba ya son ganin Mace koda 'Yar uwarsa ce. Zai rika jin tsoron magana ko gaisawa da kowacce mace koda Muharramarsa ce. 

Idan kuma Aljanar ta gagara cire wa mutum son auren daga zuciyarsa, to koda yayi auren ba zata barshi ya zauna lafiya da Iyalin ba. kullum sai fa'da ko tashin hankali. Wani ma takan hanashi saduwar aure da iyalin nasa,  Duk sanda ya matso kusa da iyalinsa sai ya rika jin faduwar gaba. Wani ma yakan dauki watanni ko shekaru bai kusanci Matarsa da saduwar aure ba. 

Akwai kuma wacce takan sanya wa mutum asara mai tsanani adukiyarsa ko wajen aikinsa duk sanda taga alamar ya fara maganar aure.  Wani kuma sukan sanya masa baqin jini mai tsanani, wato duk macen da yaje gunta sai taji ta tsaneshi. 

Irin wadannan Shaitanun suna da wahalar Sha'ani saboda wayonsu da Muguntarsu, musamman ma musulman cikinsu. Domin sun san duk wata addu'ar da za'a karanta din Qonasu. Don haka kafin a karanta aun fice daga jikin majinyacin, sai an gama su sake dawowa. 

Misalin irin wannan Akwai wani Yaro saurayi wanda muka tarar da Matayen Aljanu guda hudu ajikinsa wai suna so zasu aureshi ne.  Yanzu haka dai Allah ya taimakemu akansu dukkansu an Qonesu. Dalibanmu na Zauren Fiqhu Whatsapp zasu samu Audio na Ruqyan daga nan zuwa Yamma in sha Allahu. Zakuji irin yadda suke da taurin kai. 

Ya Allah ka kiyayemu daga Sharrukan  Shaitanun Aljanu da mutane.. 

DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990 08157968686) Anyi ainahin rubutun aranar 04-04-2017 07-07-1438. An sabuntashi aranar 16/11/2020.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI