FA'IDODIN YIN SADAQAH DAGA ZAUREN FIQHU
Ya kai 'Dan uwa Musulmi!! Ya ke 'Yar uwa Musulma!! Shin ko kun san cewa sadaqah tana da Mutukar amfani arayuwar 'Dan Adam?
Bari kuji wasu daga cikin fa'idodin dake cikinta :
1. Sadaqah wata Qofa ce daga kofofin samun shiga Aljannah.
2. Acikin dukkan ayyukan lada, Sadaqah tana daga sahun gaba. Kuma mafificiyar sadaqah ita ce "Ciyar da abinci domin Allah".
3. Sadaqah tana inuwantar da Ma'abotanta aranar Alqiyamah, Kuma tana 'Yantar dashi daga shiga Wuta. (Gwargwadon yawan sadaqarka, shine gwargwadon ni'imar da zaka shiga aranar Alqiyamah).
4. Sadaqah tana bushe fushin Ubangiji. (Allah yana son masu yinta, don haka ba zai yi fushi da kai ba).
5. Sadaqah tana kiyaye mutum daga Azabar Qabari.
6. Sadaqah ita ce mafificiyar kyautar da zakayi ma Mamacinka.
7. Sadaqah, Ubangiji ne ke rainonta har sai ranar Alqiyamah za'a nuna maka ladanta.
8. Sadaqah tana tsarkake zuciya daga Qazantar nan ta rowa da kyashi.
9. Sadaqah tana janyo maka soyayyar Allah da soyayyar Mala'ikunsa da Soyayyar bayin Allah.
10. Sadaqah tana janyo maka ninninkuwar ladan ayyukanka.
11. Sadaqah tana janyo maka hasken fuska aranar Alqiyamah.
12. Sadaqah tana janyo maka farin ciki anan duniya da kuma lahira.
13. Sadaqah tana zama dalilin yayewar damuwarka. Kuma tana kiyayeka daga bakin ciki akan abinda ya wuce.
14. Sadaqah tana kiyayeka daga Firgita aranar Alqiyamah.
15. Sadaqah tana janyo kankarewar zunubanka, da kuma gafarar laifukanka.
16. Sadaqah tana janyo ma masu yinta su samu kyakywar cikawa da imani aranar Mutuwarsu.
17. Sadaqah tana sanya Mala'ikun Allah su rika yi maka addu'ar alkhairi.
18. Masu yin sadaqah suna daga cikin mafifitan mutane awajen Allah.
19. Sadaqah tana sanya albarka acikin dukiyarka. Sannan ta tsare dukiyarka daga kowacce irin asara.
20. Sadaqah tana da albarka. Kuma da wanda ya fitar, da wanda aka wakilta ya bayar, da wanda ya mika, da wanda ya rarraba duk suna cikin ladanta.
21. Ma'abocin yawaita sadaqah, yana da alkawarin samun lada mai yawa tare da babban sakamako awajen Ubangijinsa.
22. Yana daga cikin siffofin masu tsoron Allah, zaka iske suna ciyar da dukiyarsu domin Allah,
23. Sadaqah tana daga cikin manyan alamomin Kyauta da karamci.
24. Sadaqah babbar dalili ce wajen samun karbuwar addu'o'inka, da yayewar bakin cikinka.
25. Sadaqah tana kiyaye masu yinta daga afkawa cikin bala'i.
26. Sadaqah sau daya (in dai an yita domin Allah) tana toshewa kofofi saba'in na Musibu da miyagun abubuwa tun anan duniya.
27. Sadaqah tana Qara maka tsawon rai da albarkar rayuwa da albarkar dukiya.
28. Sadaqah tana janyo maka samun nasara tare da taimakon Ubangiji acikin dukkan abinda kasa agabanka.
29. Sadaqah tana sanyawa ka samu gagarumar nasara akan Maqiyanka da mahassadanka. Kuma kaidinsu ba zai cuceka ba.
30. Idan wani ciwo yana damunka har ka rasa maganinsa, to yawaita sadaqah. In sha Allah ita Sadaqah magani ce, waraka ce, kuma kariya ce daga dukkan cututtuka.
31. Sadaqah garkuwa ce daga sharrin 'barayi, ko gobara, kuma tana kiyaye masu yinta daga mummunar cikawa.
32. Sadaqah ladanta yana tabbatuwa awajen Allah. Koda dabbobi kayi wa sadaqar, ko tsuntsaye, ko Qwaruka.
33. Babbar sadaqar da zaka fara gabatarwa ayanzu, ita ce kayi "sharing" (wato ya'da) wannan rubutun daga Zauren Fiqhu ba tare da goge koda harafi guda daga ciki ba.
Idan kayi haka da niyyar sadaqah, to duk wanda ya gani ya karanta kaima kana da lada akansa.
An gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (31-12-2016).
Comments
Post a Comment