MU SAN ANNABINMU (02)

MAHAIFANSA : Mahaifinsa shine Abdullahi 'dan AbdulMuttalibi 'dan Hashim. Yana daga mafiya kyawu da nagartar samarin zamaninsa.

Mahaifiyarsa kuwa ita ce Nana Ãminatu (Az-Zuhriyyah) 'yar Wahbin 'dan Abdu Manaf 'dan Zuhrata. Ta fito daga dangi masu tsarki da nagarta da daukaka daga cikin dangogin larabawa Quraishawa.

HAIHUWARSA :

An haifi Shugabanmu Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne a garin Makkah acikin unguwar banu Hashim, ranar litinin sha biyu (12) ga watan rabee'ul awwal ashekarar giwaye, wacce tazo daidai da 20 ga watana aprilu shekara ta 571 miladiyyah.

An haifeshi ne maraya kasancewar mahaifinsa ya riga ya rasu tun yana da 'yan watanni acikin mahaifiyarsa. Kuma an haifeshi mai tsarki mai haske mai Qamshi, idonsa da tozali. Kuma ya sauka tare da haske mai girma wanda ya haskake garin makkah baki dayansa har garuruwa masu nisa.

Kakansa Abdul Muttalibi ne ya ra'da masa wannan suna "MUHAMMADU" bisa ilhamar Ubangiji domin ya zamto abin yabo acikin sammai da Qassai (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban Annabawa da Manzanni tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa adadin dukkan halittun Allah, da iyakacin yardarsa, adadin Qurewar gudanuwar kalmominsa.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (27-10-2018 18-04-1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI