MU SAN ANNABINMU (07)
Assalamu alaikum. Wannan shine darasi na bakwai acikin tarihin Shugaban Halitta (saww) kamar yadda muka gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp.
ZAMANSA AWAJEN BAFFANSA :
Kamar yadda muka fa'da tun da farko, bayan rasuwar Kakansa sai Annabi Muhammadu (saww) ya koma hannun baffansa mai suna Abu Talib wato dan uwan mahaifinsa wanda suka fito ciki daya. Alokacin nan yana da shekaru takwas (8) kenan aduniya.
Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya taso ahannun Abu Talib cikin soyayya da mutuntawa da girmamawa, har zuwa lokacin da yayi masa aurensa na fari.
Ya zauna awajensa tare da sauran yaran gidan kuma shi yayi fiche wajen kyawun halaye da dabi'u. Ba ya yin wasa ko hayaniya irin wacce sauran yara sukeyi. Haka kuma wajen cin abinci ba ya ha'dama irin wacce yara keyi. Yana cin abinda ke gabansa ne ka'dai, kuma da zarar yaci ka'dan ya isheshi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
SANA'O'INSA (SAWW) :
Ya fara sana'a ne tun yana da shekaru takwas aduniya. Kuma farkon sana'ar da yayi aduniya ita ce sana'ar kiwon dabbobi (wato irin sana'ar Annabawa da Manzannin da suka gabaceshi kenan).
Daga nan sai kuma ya fara koyon kasuwanci ta hanyar safara (tafiye-tafiye) tare da baffansa Abu Talib alokacin yana 'dan shekara goma sha biyu. Kuma acikin irin wannan tafiyar ne suka nufi Qasar Sham inda ya ha'du da wani Malamin addinin Yahudawa mai suna Buhaira. In shaAllah adarasinmu na gaba zakuji yadda sukayi dashi.
Salati da tasleemi su tabbata ga Zababben Zababbu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka, da mabiyansa baki daya har zuwa ranar sakamako. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (07/11/2018).
Comments
Post a Comment