KUNDIN SOYAYYA (01)
Kar kuji na ambaci kalmar "Soyayya" kuyi zaton ko soyayyar wani ko wata nake nufi..
A'a ni ina nufin shiga cikin kundin soyayyar Masoyin Allah ne, Zababben Allah (saww) :
Zamu leka cikin Kundin kaunarsa domin mu karanto wasu kalmomin Soyayya da yabo wadanda suka fito daga bakin Magabata na kwarai :
1. NANA KHADIJAH BNT KHUWAILID (RA) TA CE:
"Da ache kowanne dare da rana zan samu shimfidar Annabi Sulaimanu (as) da kuma Mulkin Sarakunan Farisa, Qimarsu awajena ba zai kai koda fiffiken sauro ba.. In dai idanuna bai kasance yana kallon fuskarka ba".
"Wallahi har abada Allah ba zai Wulakantaka ba".
2. HASSANU BN THABIT (RA) :
"IDANUNA BASU TA'BA KALLON WANDA YAFIKA KYAWU BA. KUMA MATA BASU TA'BA HAIFUWAR WANDA YA FIKA KYAWU BA".
"YAYIN DA NAGA HASKENSA YA BULLO, SAI DA NA SANYA HANNUNA AKAN IDONA SABODA KWARJINI".
3. IMAM ALIYU BN ABI TALIB (RA) YACE:
"BAN TA'BA GANIN WANI IRINSA KAFINSA BA. KUMA ABAYANSA MA BANGA KAMARSA BA (SAWW)".
"TUN INA QARAMI NA SALLAMA MAKA RAINA, KUMA BA ZAN GUSHE INA SALLAMA MAKA RAINA DA DUKIYATA DA DUK WANDA KE TARE DANI DA KUMA DUKKAN ABINDA NA MALLAKA BA".
4. SAYYIDUNA ABUBAKRIN (RA) YACE :
"Dani da dukiyata ai duk naka ne Ya Rasulallahi (saww)!".
"Muna fansarka da dukiyoyinmu, Muna fansarka da rayukanmu da na iyalanmu".
"Ai 'Dan Abu Quhafah bai isa shiga gabanka ba Ya Ma'aikin Allah".
Wannan fa kadan ne daga kalmomin so da Qauna wadanda suka fito daga bakin Masoyansa na farko (saww).
Ya Allah ka Qara mana soyayya da Qauna da biyayya da sallamawa gareshi. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU (19-01-2017 21-04-1438).
Comments
Post a Comment