MU SAN ANNABINMU (08)

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da ya zamanto matattarar lamarin halittu, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah da Sahabbansa da dukkan mabiyansa har zuwa ranar tashin halittu.

HADUWARSU DA BUHAIRA :

Yayin da Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya cika shekaru goma sha biyu aduniya, sai baffansa Abu Talib ya fara tafiye-tafiyen kasuwanci tare dashi. Kuma daga cikin safarorin da yayi dashi, akwai tafiyar da sukayi zuwa Birnin Sham (wato Syria).

Yayin da suka iso wani gari mai suna Busra wanda ke kan hanyar Sham din, sai suka sauka domin hutawa awani waje, kuma anan ne wani Malamin addinin Nasaara (Kirista) mai suna Buhaira yaga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Buhaira ya kasance yana yin ibadah ne tsawon shekaru acikin wajen bautarsa, anan ne ya hangi Manzon Allah (saww) kuma ya shaidashi ya gane cewa lallai shine Annabin Qarshe, ta dalilin wasu alamomi da ya gani.

Misali ya lura da cewa Giza-gizai suna lullube wannan jama'ar matafiyan. Wato suna tafiya girgijen yana binsu.  Don haka ya shirya musu abinci kuma ya kirasu domin yin liyafa. Da suka taho gareshi gaba dayansu sai yaga girgijen bai biyosu ba. Don haka ya tambayi  Abu Talib "Shin akwai wani wanda kuka bari a baya?".

Sai yace "Eh wani yaro ne Qarami".

Sai Buhaira yayi umurni lallai azo dashi. Nan take sai ga Giragizan nan sun taho tare dashi ta samansa duk inda yabi, suna yi masa inuwa.

Sai Buhaira yace "Shin wanene Mahaifinsa?". Abu Talib yace "Nine".

Sai Buhaira yace "Bai kamata ga wannan yaron ache mahaifinsa yana nan araye ba".

Sai Abu Talib yace "Gaskiya ni baffansa ne".

Anan sai Buhaira ya umurci Abu Talib cewa lallai ya koma ya mayar da Annabi (saww) gida. Domin hakika shine Annabin Qarshe. Kuma lallai idan har suka Qarasa shiga Birnin Sham, Maluman yahudawa da nasaaran dake chan zasu ganeshi domin alamomin Annabtar dake tare dashi. Idan kuwa har suka ganeshi to sai sunyi yunkurin kasheshi.

Don haka baffansa nasa ya koma dashi garin Makkah, Kuma bai sake tafiya dashi wata Qasa mai nisa ba.

SALATI DA TASLEEMI SU TABBATA BISA ANNABIN RAHMA MA'ABOCIN FALALA DA FIFIKO TARE DA IYALAN GIDANSA TSARKAKA SALATIN DA ZAI ZAMANTO SILAR SAMUN DARAJA DA FIFIKO GAREMU ARANAR ALKIYAMAH. AMEEN.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 07064213990 (01/03/1440  09/11/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI