IMAM MUHAMMADUL BAQIR (RTA)


Yau ma muna tare da wani jigo ne daga jiga-jigan al'ummar gidan Annabta (Ahlul Baiti).

Sunansa Muhammad, irin sunan Kakansa na farko kenan (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Sunan Mahaifinsa Aliyu bn Alhusain wanda ake yiwa laqabi da Zainul Abideena.

Mahaifiyarsa ita ce Ummu Abdillahi, Fatimah 'yar Imamul Hasan Almujtabah (amincin Allah ya tabbata garesu da dukkan Ahlul Baiti baki daya) .

Ana yi masa Alkunya da Abu Ja'afar  (saboda 'dansa Ja'afarus Sadiq). Kuma saboda zurfin iliminsa ana yi masa laqabi da "BAQIRUL ULUM" (Mai yalwar Ilimi, mai tsage Ilimai, rumbun ilimai).

An haifeshi aranar Talata 3 ga watan Safar shekara  ta 57 bayan Hijirar Kakansa (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Shekarunsa uku aduniya lokacin da aka shahadantar da Kakansa Imamul Husaini (yardar Allah ta tabbata garesu baki daya).

Ya rasu kuma aranar 23 ga watan Safar shekara ta 114 bayan Hijira.  Wasu kuma sun ce ya rasu ne ashekara ta 117. Wasu kuma sun ce shekara ta 113.

Ya rasu ne awani gari da ake kira Hameemah (ko Humaimah) sannan aka dauko gawarsa aka dawo da ita garin Madeenah, aka binneshi a makabarta Baqee'a acikin Qabarin da aka sanya Mahaifinsa (Zainul Abideen) da kuma Baffan Mahaifinsa (Imamul Hasan) kuma acikin Qubbar da Qabarin Sayyiduna Abbas 'dan Abdul Muttalibi yake (radhiyallahu anhu).

Shine farkon wanda aka haifa Bahashimi kuma Alawiy, domin Mahaifansa dukkansu hashimawa ne kuma 'Alawiyyai. Shine irinsa na farko aduniya.. Mahaifinsa 'dan Imamul Husaini ne. Mahaifiyarsa kuma 'yar Imamul Hasan. Wato ta ko ina shi 'dan gidan Nana Fatimah ne da Sayyidi Aliy (yardar Allah ta gamesu baki daya).

Shine dalilin da ake ce masa Al'alawiy Al-Fatimiy (radhiyallahu anhu).

Ya ruwaito hadisai Maraseel daga Annabi (saww) da kuma Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (rta). Yana da wasu Maraseel din ta hanyar Imamul Hasan da Imamul Husaini (radhiyallahu anhuma).

Da kuma wasu hadisan su ma Maraseelu ta hanyar Nana A'ishah, Nana Ummu Salamah, da Sayyiduna Abdullahi bn 'Abbas (radhiyallahu anhum).

Yayi karatu wajen Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy, Abu Sa'eed Alkhudriy, Abdullahi bn Ja'afar, Abu Hurairah, Samurah bn Jundub, Sa'eedu bn Almusayyib (rta).

Kuma ya karbi zurfafan Ilimai awajen Mahaifinsa Aliyu Zainul Abideen, da Baffansa Muhammad ibnul Hanafiyyah (ra).

Daga cikin Almajiransa kuma akwai 'dansa Ja'afarus Sadiq, 'Ata'u bn Abi Rabahin, da Al A'araju, da Amru bn Deenar, da Ibnu Shihab Azzuhriy (Malamin Imamu Malik).

Cikin Almajiransa dai akwai irin su Abu Is'haq As-Subai'eey, Yahya bn Abi Katheer, Rabee'ah, Ibnu Juraij, da A'amash, Ibnu Arta'ah, da sauransu. Kuma akwai hadisansa acikin Sunanun Nisa'iy da sunanu Abi Dawud.

Zahabiy yana magana akansa acikin littafinsa mai suna Siyaru A'alamin Nubala',  yace : "Imam Muhammadul Baqir yana daga cikin mutanen da suka ha'da tsakanin Ilimi da aiki dashi, da Shugabanci da daukaka da aminci da kaifin basira.... Yana daga cikin Imamai goma sha biyu wadanda 'yan shi'a ke cewa Ma'asumai ne. Amma babu Isma sai ga Mala'iku da Annabawa (alaihimus salam)".

Kuma kowanne mutum yana iya yin daidai, kuma yana kuskure. Kuma ana iya karbar zancensa ko a mayar masa. In banda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Ya shahara sosai ta wajen karatun Alqur'ani (Qira'ah). Kuma almajirinsa Salim bn Abi Hafsah ya tambayeshi game da Sayyiduna Abubakar da Sayyiduna Umar (ra) sai yace "Ya kai Salimu kaso su kuma kayi bara'ah daga Qiyayyarsu. Domin su shuwagabannin Shiriya ne".

Anan zamu tsaya sai wani karon da fatan Allah shi Qara mana son Annabi (saww) da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan Salihan bayin Allah baki daya.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (06/08/2018  24/11/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI