ANNABINA SHUGABANA MACECINA (SAWW)

ANNABINA, MASOYINA (SAWW) SHINE :
*****************************************
DHU QUWWATIN : Ma'abocin Qarfin jiki da Qarfin Hujjah. Annabin da shi kadai yaci nasarar da sauran Annabawan Allah vasu samu ba. Ya kori shirka,  ya karya gumaka, ya tsarkake Ka'abah.

DHU HURMATIN : Ma'abocin alfarma aduniya da lahira. Annabin da saboda shi Allah yake dauke Bala'i, kuma yake saukr da niimah.  Shine wanda saboda alfarmarsa al'ummarsa ta samu daukaka da darajoji.

DHU MAKANATIN : Ma'abocin Qurewar Matsayi afadar Allah. Shine wanda Allah ya tara dukkan Annabawa sukayi imani dashi, sukayi masa chaffa, Suka dauki alkawarin taimakonsa wajen isar da sako.

DHU 'IZZIN : Ma'abocin Buwaya aduniya da lahira. Shine wanda ya chusa tsoro da razana azukatan Sarakunan duniya tun afarkon lokacin bayyanarsa.

DHU FADHLIN : Ma'abocin Falala da fifiko a saman dukkab halittu. Shine wanda ambaton sunansa yake yaye damuwa ga Masoyansa.

Kallon fuskarsa yakan Gigita hankali,  Tunaninsa da begensa sukan ratsa zuciyar Ma'abota Qaunarsa har ido ya zubda hawaye.

Ya Allah yi salati da girmamawa agareshi tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa da Mabiyansa har zuwa ranar Sakamako.

DAGA ZAUREN FIQHU (10-10-1437) 15-07-2016.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI