ALLAH YAFI GABAN KWATANCE

Hakika Allah Madaukakin Sarki, Samamme ne tun gabannin samuwa. Kuma dawwamamme ne ba tare da farko ko Qarshe ba. Babu Jihar da take ritsashi, kuma babu wajen da ake rasashi.

Shi Makadaici ne wanda Qirge ko lissafi basu riskarsa. Yafi gaban kwatance da zuciya ko tunanin masu tunani.

Bai haifa ba, kuma ba'a haifeshi ba. Shine abin nufin dukkan halittu. Kuma babu wani kini agareshi.

Bai yi kama da komai ba, kuma babu abinda yayi kama dashi. Shi Mawadaci ne ba ya bukatar komai awajen kowa, shine wanda kowa ke bukatar komai awajensa.

Mai cikakken iko ne wanda ikonsa bai rataya da zamani ko makani ba. Kuma mai nufi ne ga dukkan abinda yaso. Babu mai tambayarsa akan abinda yayi, kuma babu mai tuhumarsa akan abinda bai so kasantuwarsa ba.

Shi Masani ne tun gabannin komai. Shi yasan komai, kuma ya san kowa. Amma babu wanda ya sanshi sai shi kansa.

Shi Rayayye ne tun gabannin dukkan rayayyu. Kuma shi rayayyen bayan macewar dukkan rayayyu. Rayuwarsa bata ratayu da komai ba. Kuma bata dogara da komai ba.

Yana ji, ba ji irin na kunne ba. Yana gani ba gani na idanu ba. Kuma babu abinda ke boyuwa agareshi acikin duhun Qassai ko cikin zurfin ruwa.

Masanin fili ne da boye. Mabudan gaibu duk nasa ne, babu wanda ya sansu sai dai Shi. Kuma ya san abinda ke doron Qasa da wanda ke cikin kogi. Babu wata ganyen bishiya da zata fado fache sai ya san da ita. Babu wani danyen abu ko busashe fache sai yana cikin wani littafi mabayyani.

Yana magana ba magana irin ta harshe ba. Babu farko ko karshe ga zancensa. Kuma babu Qarshen Qidayuwa ga kalmominsa.

Koda ache dukkan bishiyoyin dake doron Qasa zasu zamanto alkalamai, kuma dukkan ruwan cikin teku ya zama shine tawadar rubutun, bayan shima a Qaro da ruwan wasu tekunan guda bakwai ba zasu iya kaiwa Qarshen rubuta kalmomin Allah ba.

Mulki da iko da sarauta da Tsarki da martaba da buwaya duk naka ne, gareka suke Ya Allah..

Kasan dukkan bukatuna koda ban furta ba.. Yi salati da Martaba da aminci ga zababben bawanka Shugabana Annabina Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa adadin abinda ke cikin iliminka.

DAGA ZAUREN FIQHU 09094623006 08163621213 07064213990 (11-11-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI