MU SAN ANNABINMU (25)

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa shiryayyu.

YAQIN BANU QAINUQA'A :

Banu Qainuqa'a sunan wata Qabila ne daga cikin Qabilun yahudawan madeenah wadanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya qulla alkawarin zan lafiya dasu tun farkon zuwansa garin.

Nasarar da Manzon Allah (saww) ya samu a yaqin badar ta basu haushi, don haka sai suka fito fili suna bayyana qiyayyarsu ga Musulmai da kuma soyayyarsu ga mushrikan Quraishawa. Kuma sun kasance suna gadara da Qarfin tattalin arziki kasancewarsu masu sana'ar zinare ne.

Suna cin mutuncin jama'ar musulmai, suna yi musu izgili har dai watarana suka yiwa wata mace musulma tsirara a kasuwarsu, ta nemi taimako awajen wani musulmi ya taimaka mata ya kashe bayahuden da ya zalunceta. Sai sauran yahudawan suka taru akansa (shi Musulmin) suka kasheshi.

Wannan shine tushen yaqin. Kuma Manzon Allah (saww) ya fita zuwa garesu aranar 2 ga watan shawwal acikin shekara ta biyu bayan hijirah (kimanin makonni biyu kenan da gama yaqin badar).

Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da Sahabbansa suka kewaye unguwar yahudawan har tsawon kwanaki goma sha biyar, da yahudawan suka ji wahala sai suka mika wuya gareshi. Don haka aka koresu daga garin Madeenah saboda sakamakon abinda suka kasance suna aikatawa.

YAQIN SAWEEQU :

Aranar biya {5} ga watan Dhul Hijjah acikin wannan shekara ta biyu din bayan hijirah sai mushrikan Makkah suka yi wani mummunan shiri aboye. Abu Sufyan ya fito tare da wasu mushrikai 200 suka taho suka kawo hari a gefen garin Madeenah, suka kashe mutum biyu daga cikin Al Ansar (mutanen madinah) kuma suka Qona gidaje biyu tare da wasu dabinai.

Yayin da Manzon Allah (saww) ya shirya domin fita garesu sai suka gudu. Yayin da suka fara tunanin kamar za'a riskesu sai suka rika jefar da kayan guzurinsu na abinci. Shi ake kira "saweeq" din. Wani abu ne da larabawa ke dama farau-farau dashi.

Annabi (saww) kwana biyar yayi ayayin wannan fitar.

YAQIN UHUDU :

An gudanar da yaqin ne akusa da dutsen nan mai suna Uhudu wanda ke kusa da garin madinah, acikin watan shawwal acikin shekara ta uku bayan hijirah.

Kuma musabbabin yaqin shine su mushrikan Quraishawa basu gushe suna jin haushin abinda ya faru akansu a yakin badar ba
Don haka suka fito awannan lokacin domin mayar da martani. Sun taho da mayaka dubu uku (3,000).

Su kuwa jama'ar da Annabi (saww) ya fita tare dasu su dari bakwai ne (700) kuma ya ware wasu maharba guda hamsin, ya umurcesu da zama akan wani dutse, kada su sauko sai sun samu umurnin yin haka daga gareshi.

An fara gumurzu, kuma nasara ta kasance ga musulmai. Har mushrikan sun fara tserewa, sai wadancan maharban sukayi tsammanin kamar an gama yaqin ne, don haka mafiya yawansu suka sauko daga wajen da Annabi (saww) ya ajiyesu.

Su kuwa mushrikan har sun fara gudu sai Khalid bn Walid (sannan bai musulunta ba) ya jagorancesu suka zagayo ta bayan dutsen suka kashe sauran maharban da suka ragu awajen, sannan suka yiwa musulmai Qawanya suka rika kashesu, mushrikai sukayi rinjaye saboda sa'ba wa umurnin Annabi (saww) da muminai sukayi.

A bangaren kafirai an kashe guda ashirun da biyu, abangaren muminai kuma mutum saba'in (70) ne sukayi shahadah acikinsu har da baffan Manzon Allah (saww) wato Sayyiduna Hamzah 'dan AbdulMuttalibi , da Abdullahi 'dan Jahshin, da Mus'abu 'dan Umairu da Sa'adu 'dan Rabee'u (Allah ya yarda dasu baki daya).

Shi kansa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya samu raunuka awajen wannan yaqin. Kuma wannan ya zamo babban darasi ne ga al'ummar musulmai cewa duk lokacin da aka sa'ba umurnin Shugaba to lallai Allah yakan jarrabi al'ummah da abinda basu ta'ba tsammaninsa ba.

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya.

An gabatar da karatun a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 07064213990 (17/04/2019 11/08/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI