YAU CE RANAR YAKIN BADAR
Wannan rana ta 18 ga Ramadhan tana daga cikin ranakun tarihi wadanda bai kamata duk wani musulmi ya manta dasu ba.
Kamar shekaru 1434 da suka gabata, awannan ranar kafiran Makkah suka fito da manyan Jarumansu da Manyan Masu Hannu da shuninsu.. Gaba dayansu su 1000 (dubu daya). Duk sun fito da kayan yakinsu sun taho domin su Murkushe Musulmai da Musulunci.
Shi kuma ANNABI (saww) ya fito tare da Sahabbansa 'yan kadan, su 313 ne. Kuma babu wani cikakken shirin Yaki ko manyan Makamai sosai tare dasu..
Daga Bangaren Dakarun Kafirai akwai manyan kwamandodi irin su:
- Abu Jahal bn Hisham.
- Shaibatu Bn Rabee'ah.
- Utbatu Bn Rabee'ah.
- Umayyatu bn Khalaf.
Daga Bangaren rundunar Musulmai kuma, babban kwamandansu shine SAYYIDUNA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW). Amma a karkashinsa akwai Manyan Kwamandodi kamar su:
- Zakin Allah da Manzonsa (Hamzatu bn Abdil Muttalib).
- Aliyyu Bn Abi Talib (ra).
- Zubair bn Al-awwam (ra).
- Umar bn Alkattab (ra).
ALLAHU AKBAR!!! Ya Allah ka saka ma Sahabban nan da alkhairi... Ya Allah ka qara musu yarda!!! Yadda suka fito suka sayar maka da ransu domin kariyar Manzonka da addininka da yazo dashi, Ya Allah ka tsine ma dukkan Makiyinsu!!!
Yau gaba dayan Post din ZAUREN FIQHU zamu yishi ne akan details na yakin Badar.. Kuma mun sadaukar da wannan ranar ne domin SAHABBAN DA SUKA HALARCI YAQIN BADAR. (Har da Sayyiduna Uthman bn Affan wanda bai samu zuwa ba, saboda ya tsaya jinyar matarsa 'Yar Manzon Allah saww).
Comments
Post a Comment