DAGA TASKAR AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)

IMAM JA'AFAR ASSADIQ (RTA) YACE:

"Ina mamakin mutumin da yake cikin tsoro amma bai dukufa cikin karanta "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL" ba.

Ina mamakin mutumin da Bakin ciki ya dameshi amma bai karanta "LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEENA" ba.

"Ina mamakin Mutumin da Masu Makirci suka dameshi da Makirci amma bai karanta "WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI' ba".

Ni kuma Mai Zauren Fiqhu na Qara da cewa :

"Ina mamakin mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, amma bai yawaita karanta "ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA' ba".

"Ina mamakin mutumin da yake neman haihuwa amma bai yawaita "RABBEE HABLEE MIN LADUNKA DHURRIYYATAN TAYYIBAH, INNAKA SAMI'UD DU'A'I ba".

"Ina mamakin mutumin da talauci ya dameshi amma bai yawaita Istighfari da Salatin Annabi (saww) ba.

Ina mamakin mutumin da ya shiga matsala amma bai yawaita LA HAULA WALA ƘUWWATA ILLA BILLAHIL 'ALIYYIL 'AZEEM ba".

"Ina Mamakin Mutumin da yaga wannan saƙon amma bai yi aiki dashi ba, Kuma bai tura ma sauran 'Yan uwa Musulmai don su amfana ba".

Ina mamakin ƁARAYIN FASAHA masu satar rubutun Mutane Kuma su goge ainahin sunan mai rubutun sannan su sanya nasu..Suna zaton Allah bai sansu ba".

DAGA ZAUREN FIQHU (17-05-2016) 07064213990.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI