Posts

MADUBIN DUBAWA (64)

Sa'eed bn Sulaiman yace "Na kasance acikin garin Makkah tare da Abdullahi bn AbdilAzeez  Al Umariy ('Daya daga cikin Maluman Tabi'ai masu gudun duniya). Alokacin nan Khalifah Harunar Rasheed yazo wajen aikin hajji. Sai wani mutum yace wa Abdullahi Al Umariy, "Ya kai baban Abdurrahman! Gashi chan Sarkin Muminai (Harunar Rasheed) yana Sa'ayi (wato tafiya tsakanin Safa da Marwah) kuma duk an bar masa wajen sa'ayin!". Sai shi Abdullahi Al Umariy din yace ma mutumin "Kada Allah ya saka maka da alkhairi domin ka dora min wani aiki wanda na wadatu da barinsa". Sai ya tashi ya dauki takalmansa ni kuwa ina binsa abaya. Sai ga Harunar Rasheed ya taho daga Marwah ya nufi Safaah.. Sai Abdullahi Al Umariy yayi kiransa yace "YA KAI HAROON!". Da khalifan ya waiwayo ya ganshi sai yace "Amsawarka Ya baffana!". Sai yace "Mu hau dutsen Safaa". Yayin da suka hau sai yace ma Khalifan "Sanya idanuwanka wajen 'Dakin All...

FA'IDODIN YIN SADAQAH (DAGA ZAUREN FIQHU)

Ya kai 'Dan uwa Musulmi!! Ya ke 'Yar uwa Musulma!! Shin ko kun san cewa sadaqah tana da Mutukar amfani arayuwar 'Dan Adam? Bari kuji wasu daga cikin fa'idodin dake cikinta : 1. Sadaqah wata Qofa ce daga kofofin samun shiga Aljannah. 2. Acikin dukkan ayyukan lada, Sadaqah tana daga sahun gaba. Kuma mafificiyar sadaqah ita ce "Ciyar da abinci domin Allah". 3. Sadaqah tana inuwantar da Ma'abotanta aranar Alqiyamah, Kuma tana 'Yantar dashi daga shiga Wuta. (Gwargwadon yawan sadaqarka, shine gwargwadon ni'imar da zaka shiga aranar Alqiyamah). 4. Sadaqah tana bushe fushin Ubangiji. (Allah yana son masu yinta, don haka ba zai yi fushi da kai ba). 5. Sadaqah tana kiyaye mutum daga Azabar Qabari. 6. Sadaqah ita ce mafificiyar kyautar da zakayi ma Mamacinka. 7. Sadaqah, Ubangiji ne ke rainonta har sai ranar Alqiyamah za'a nuna maka ladanta. 8. Sadaqah tana tsarkake zuciya daga Qazantar nan ta rowa da kyashi. 9. Sadaqah tana janyo maka soyayyar ...

RANAR HAIHUWARSA (SAWW)

Ko kasan cewa yayin da Nana Ãminatu bintu Wahbin ta dauki cikin Manzon Allah (saww) ta kasance akowanne dare na watannin goyon cikin tana ganin Annabawa da Manzanni (alaihimus salam) suna zuwa gareta suna gaisuwa tare da yi mata albishirin cewa zata haifi Shugabansu baki daya (saww). Ko kasan cewa alokacin da aka haifi Manzon Rahama (saww) akwai wani gagarumin hasken da ya fito tare dashi, tun daga garin Makkah har sai da ya haskaka manyan Katangun garuruwan Qasar Sham.. Ko kasan cewa Shi komai nasa daban yake, ranar haihuwarsa anji muryoyi daban daban suna yin murna da zuwansa. A daren saukarsa duniya, an wayi gari dukkan kujerun sarakunan duniya sun kife, Hakanan dukkan gumaka da kayan tsafi sun wayi gari kife akan fuskokinsu. Ya kasance shine mafi kyawun mutane, kuma mafi daidaiton halitta. Jikinsa yana haske, fatarsa tana Qamshi, hakoransa suna haske. Bashi da inuwa, Qura bata sauka ajikinsa, Quda ba ya hawa kan fatarsa, Kuma idan yana tafiya akan rairayi ba'a ganin alamar ...

YADDA AKE KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH.

Idan kana tunanin anyi maka sihiri ko anyi ma wani 'Dan uwanka, Ko kuma matsalar Maita (Kambun Ido) to ga hanya mai sauki kuma halastacciya wacce Zauren Fiqhu ya dauko daga cikin irin fatawoyin da muke amsawa akan shafukanmu na Internet. Da farko dai dole ka sanya hakuri da Tawakkali da tsoron Allah acikin zuciyarka. Ka fidda Qiyayya ko zargi atsakaninka da duk wani Musulmi. Sannan ka aikata wannan fa'idar : 1. Asamu ruwa cikin Bokiti, ka samo ganyen Magarya guda 7 ka dandakasu akan dutse da dutse sannan ka zuba acikin ruwan. Ka tsoma babban yatsan hannunka na dama acikin ruwan. Ka kusanto da bakinka daf da ruwan. Sannan ka karanta wadannan ayoyi da surorin : 1.  Fatiha. 2. Suratul Baqarah ayah ta 1-5. da kuma ayah ta 102-103. da kuma ayah ta 163-164. Da kuma ayah ta 255 - 257. Da kuma 285-286. 3. SURATU AALI 'IMRAAN : Ayah ta 18-19. 4. SURATUL A'ARAF : 54-56. da kuma 117-122. 5. SURATU YUNUS (AS) : Ayah ta 81-82. 6. SURATU TAAHA (AS) : Ayah ta 69. 7. SURATUL ...

MATSAYIN SAYYIDUNA ABUBAKAR (RADHIYALLAHU ANHU) AWAJEN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM).

Hakika alaqar dake tsakanin Ahlul Baiti da manyan Sahabban Manzon Allah (saww) alaqah ce dake kunshe da mutukar Qauna da girmamawa tare da kulawa da hakkokin juna. Sahabbai suna girmama Ahlul baiti saboda kusancinsu da Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) su kuma Ahlul Baiti suna girmama Sahabbai saboda yardar da suka samu awajen Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da taimakon da sukayi wa addininsa. Muhammad Ibnul Hanafiyya, daya daga cikin 'ya'yan Sayyiduna Aliyyu (rta) kuma Kogin ilimi, babban Malami acikin Tabi'ai, yace "Na Tambayi Mahaifinmu "Shin wanene mafi alkhairin mutane, bayan Manzon Allah (saww)? Sai yace min "Abubakar" Nace sannan sai wa? sai yace "Umar." Ina jin tsoron kar yace sai Uthman. sai nace masa sannan sai kai? Sai yace min "A'a.. ni dai daya ne daga cikin al'ummar Musulmi". (Bukhary juzu'i na 7, shafi na 24. hadisi mai lamba 2,671). Duk da cewa ya faÉ—i...

LABARI MAI BAN-TSORO

Qissah ce daga Shaikh Abdullahi bn Ahmad Al-Mu'azzin (rah) yace : "Na kasance ina yin 'Dawafi a dakin Ka'abah sai naga wani Mutum (Dattijo) ya Qanqame rigar Ka'abah yana Tsula kuka yana addu'a yana cewa : "YA ALLAH KA FITAR DANI DAGA DUNIYAR NAN INA MUSULMI". Yana fa'da yana Maimaitawa kuma ba ya Qara komai akan haka. Sai nace masa "Ya Kai Bawan Allah! Shin ba zaka Qara komai akan wannan ba?". Sai ya juyo gareni yace "Da ache kasan labarina da ba zaka ce haka ba". Sai nace "Menene labarin naka?". Sai yace "Na Kasance ina da 'Yan uwa Maza guda biyu. Babban cikinsu ya kasance shi Ladani ne (Mai Kiran Sallah). Yayi shekaru Arba'in (40) yana kiran sallah don neman lada. Amma yayin da Mutuwa tazo gareshi sai ya bukaci mu kawo masa Mus'hafi (Wato Alqur'ani cikakke). Har muna Tsammanin cewa watakil zai yi Tawassuli dashi ne domin neman albarka. Amma yayin da ya karbi Alqur'anin ya rikeshi da hann...

FALALAR AZUMIN ASHURA (DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP)

Wannan cikakken bayani ne daga ZAUREN FIQHU dangane da Azumin Tasu'ah da Ashurah. Hakika ranar ashura, rana ce wacce babu irinta acikin ranakun shekara baki daya. Domin kuwa rana ce wacce manyan Muhimman al'amura na tarihi suka faru acikinta. Rana ce wacce addinin Musulunci ya sunnanta yin azuminta domin koyi da Manzon Allah (saww). Kamar yadda zamu gani acikin hadisai Sahihai masu zuwa in sha Allahu. Daga Abu Hurairah (ra) yace "An tambayi Manzon Allah (saww) "Shin wacce Sallah ce tafi falala bayan Sallolin farillah?". Sai yace ".YIN SALLAH CIKIN TSAKAR DARE". Sai aka ce "Wanne Azumi ne yafi falala bayan na Ramadhan?" Sai yace: "WATAN NAN NA ALLAH WANDA KUKE KIRANSA ALMUHARRAM". (Muslim da Ahmad da Abu Dawud ne suka ruwaitoshi). Kunga wannan hadisin ya nuna mana cewa falalar wannan azumin da akeyi acikin Almuharram wato Ashura da Tasu'ah kenan sun zarce falalar yin azumi awani watan  in banda Ramadhan. Daga Sayyiduna Mu...