MADUBIN DUBAWA (64)

Sa'eed bn Sulaiman yace "Na kasance acikin garin Makkah tare da Abdullahi bn AbdilAzeez  Al Umariy ('Daya daga cikin Maluman Tabi'ai masu gudun duniya). Alokacin nan Khalifah Harunar Rasheed yazo wajen aikin hajji.

Sai wani mutum yace wa Abdullahi Al Umariy, "Ya kai baban Abdurrahman! Gashi chan Sarkin Muminai (Harunar Rasheed) yana Sa'ayi (wato tafiya tsakanin Safa da Marwah) kuma duk an bar masa wajen sa'ayin!".

Sai shi Abdullahi Al Umariy din yace ma mutumin "Kada Allah ya saka maka da alkhairi domin ka dora min wani aiki wanda na wadatu da barinsa".

Sai ya tashi ya dauki takalmansa ni kuwa ina binsa abaya. Sai ga Harunar Rasheed ya taho daga Marwah ya nufi Safaah.. Sai Abdullahi Al Umariy yayi kiransa yace "YA KAI HAROON!".

Da khalifan ya waiwayo ya ganshi sai yace "Amsawarka Ya baffana!".

Sai yace "Mu hau dutsen Safaa".

Yayin da suka hau sai yace ma Khalifan "Sanya idanuwanka wajen 'Dakin Allah".

Yace "Nayi".

Sai yace "Su nawa ne adadinsu?" (Yana nufin mutanen dake yin dawafi awajen).

Sai Khalifah Harunar Rasheed yace "Waye ya isa yasan adadinsu!".

Sai Umariy yace "To mutane kamar haka ninki nawa ne akarkashin mulkinka?".

Sai yace "Jama'a ne masu yawa babu wanda yasan iyakarsu in banda Allah".

Sai Umariy "To ka sani yakai wannan Sarki, hakika kowanne daga cikinsu (aranar lahira) za'a tambayeshi ne game da kansa ka'dai. Amma kai din nan kai 'daya sai an tambayeka game da kowannensu. Yi tunani kaga yaya zaka kasance!!".

Nan take Harunar Rasheed ya fashe da kuka, ya zauna yana ta kuka hawayensa yana kwarara, mutanensa suna ta miko masa hankici bayan hankici yana ta jikesu da hawayensa.

Sai Abdullahi Al Umariy ya tashi ya mike yace masa "Akwai wata maganar da zan sake fa'da".

Yace "Ka fa'deta kawai Ya Baffana!".

Sai yace "Ina rantsuwa da Allah hakika mutum yakan juya dukiyarsa ta kansa amma azaba ta chanchanta akansa.. To yaya kuma wanda ke juya dukiyar Gwamnatin al'ummar Musulmai??".

Da ya gaya masa wannan sai ya juya ya tafi, ya bar Harunar Rasheed a tsugune yana ta zabga kuka!! 😭😭😭.

Bayan kun karanta wannan Qissar ya kamata ku san wanene Khalifah Harunar  Rasheed (rah).

Yana daga cikin manyan Sarakunan Daular Banul Abbas wadanda suka dafe madafan ikon al'ummar Musulmai tun bayan shudewar daular Banu Umayyah.

Yankin da ya mulka azamaninsa ya kunshi Qasashe kamar haka : - Saudi Arabia, Bahrain, Oman, Qatar, Jordan, Yemen, Syria, Egypt, Kuwait, Iraq, Iran, UAE, Palestine, Afganistan, Azberjan, Turkey, da sauransu.

Yana mulkin kusan nahiya (Continent) guda, Kuma yana da sojoji da dakaru Miliyoyi da bayi da kuyangi daruruwa ga kuma tarin kudaden dake karkashin ikonsa amma wannan Malami ya fito Qarara yayi masa wa'azi ba tare da jin tsoro ba. Shi kuma ya karbi wa'azin har ya ratsa masa zuciya yake ta sheqa kuka.

Ku dubi yanayin Malaman Zamani yadda suka zama 'Yan amshin shatan Azzaluman shugabanni!!!. Babu Malamin da zai tafi fadar gwamnati musamman don yiwa Chiairman ko Gwamna ko President wa'azi..

Babu Malamin da zai gayyaci 'yan Majalisun Jiha ko na tarayya domin yayi musu wa'azi akan hanyoyin da zasu bi su taimaki talakawansu domin sauke nauyin da Allah ya dora musu!!!

Sai dai a wuraren tafseerai su rika kafirta junansu suna rarraba kan al'ummah.. Kuma tsakaninsu da Shugabanni sai dai su rika cika musu account dinsu da kudaden jama'a suna cinyewa.

Ya Allah ka jikanmu ka gafarta mana laifukanmu ka sanyamu cikin bayinka nagartattu don falalarka da rahamarka ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (27/09/2018 17/01/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI