RANAR HAIHUWARSA (SAWW)

Ko kasan cewa yayin da Nana Ãminatu bintu Wahbin ta dauki cikin Manzon Allah (saww) ta kasance akowanne dare na watannin goyon cikin tana ganin Annabawa da Manzanni (alaihimus salam) suna zuwa gareta suna gaisuwa tare da yi mata albishirin cewa zata haifi Shugabansu baki daya (saww).

Ko kasan cewa alokacin da aka haifi Manzon Rahama (saww) akwai wani gagarumin hasken da ya fito tare dashi, tun daga garin Makkah har sai da ya haskaka manyan Katangun garuruwan Qasar Sham..

Ko kasan cewa Shi komai nasa daban yake, ranar haihuwarsa anji muryoyi daban daban suna yin murna da zuwansa.

A daren saukarsa duniya, an wayi gari dukkan kujerun sarakunan duniya sun kife, Hakanan dukkan gumaka da kayan tsafi sun wayi gari kife akan fuskokinsu.

Ya kasance shine mafi kyawun mutane, kuma mafi daidaiton halitta. Jikinsa yana haske, fatarsa tana Qamshi, hakoransa suna haske. Bashi da inuwa, Qura bata sauka ajikinsa, Quda ba ya hawa kan fatarsa, Kuma idan yana tafiya akan rairayi ba'a ganin alamar takun Qafarsa. Amma idan yana tafiyua bisa dutse anan ne tafin Qafarsa ke bayyana (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Daga cikin matayen da suka halarci gidan Nana Ãminatu bintu Wahbin yayin haihuwar nan akwai Shaffa'u mahaifiyar Sayyiduna Abdurrahman bn 'Auf (rta) da kuma Ummu Ayman,  Barakatul Habashiyyah (rta) dukkansu sun bada shaidar abubuwan mamakin da suka gani da idonsu.

Don Qarin bayani aduba :

- KITAABUS SIRAH NA IBNU HISHAM.

- AL BIDAYAH WAN NIHAYAH NA IBNU KATHEER.

- SIRATUL HALBIYYAH NA IMAMUL HALBIY.

- DALA'ILUN NUBUWWAH NA BAIHAQIY.

Ya Allah kayi dubunnan salati da aminci bisa Shugaban dukkan bayinka Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa masi girma, da dukkan Salihan bayinka ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 07064213990 (14/01/1440  24/09/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI