MATSAYIN SAYYIDUNA ABUBAKAR (RADHIYALLAHU ANHU) AWAJEN AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM).

Hakika alaqar dake tsakanin Ahlul Baiti da manyan Sahabban Manzon Allah (saww) alaqah ce dake kunshe da mutukar Qauna da girmamawa tare da kulawa da hakkokin juna.

Sahabbai suna girmama Ahlul baiti saboda kusancinsu da Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) su kuma Ahlul Baiti suna girmama Sahabbai saboda yardar da suka samu awajen Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da taimakon da sukayi wa addininsa.

Muhammad Ibnul Hanafiyya, daya daga cikin 'ya'yan Sayyiduna Aliyyu (rta) kuma Kogin ilimi, babban Malami acikin Tabi'ai, yace "Na Tambayi Mahaifinmu "Shin wanene mafi alkhairin mutane, bayan Manzon Allah (saww)?

Sai yace min "Abubakar"

Nace sannan sai wa? sai yace "Umar."

Ina jin tsoron kar yace sai Uthman. sai nace masa sannan sai kai?

Sai yace min "A'a.. ni dai daya ne daga cikin al'ummar Musulmi".

(Bukhary juzu'i na 7, shafi na 24. hadisi mai lamba 2,671).

Duk da cewa ya faɗi hakan ne bisa tawadhu'u (Qankan da kai) irin nasa, to amma hakan yana nuna yadda sauran sahabbai suke da matsayi agunsa.

Abdullahi bn Salamah yace: "Naji Sayyiduna Aliyu (karramal Lahu Wajhahu) yana cewa :

"MAFIYA ALKHAIRIN MUTANEN (wannan al'ummah) BAYAN MANZON ALLAH (saww) SUNE ABUBAKAR DA UMAR"

Kuma ya kasance yana cewa:

"IDAN AKA ZO MIN DA WANI MUTUMIN DAKE FIFITANI AKAN ABUBAKAR DA UMAR, SAI NAYI MASA HADDIN QAZAFI (BULALA 80).

Yawancin wadannan Maganganun, Sayyiduna Aliyu (rta) yana fadarsu ne akan Mimbari acikin garin Koufah domin gyara tarbiyyah al'ummah da toshe ɓaraka.

Kuma yana yin hakane domin magance matsalar masu kawo shubuha da rikici acikin addinin Allah. Tare da bayyana ma duniya cewa shi dai yayi bara'a daga masu zagin Wasu Sahabbai, wai kuma suna danganta kansu gareshi..

1. Waccan Hadisin na 2, Ibnu Maajah ne ya ruwaito shi acikin Muqaddimarsa acikin babin Falalar Sahabbai. juzu'i na 1, shafi na 39, hadisi na 106.

Kuma an ruwaitoshi ta hanyoyi sama da 80,  Imam Ahmad ma ya kawoshi acikin Musnad nashi awurare da dama. aduba hadisai masu lamba: 128-139, da na 397, 412, 413, 414, 429, da 430.

Wannan na ukun kuma aduba Musnadu Ahmad hadisi na 189 da kuma na 387.

Anan zamu tsaya sai a karatu na biyu in sha Allahu zamui dora daga inda muka tsaya.

YA ALLAH KA GANAR DA WADANDA BASU GANE BA..

DAGA ZAUREN FIQHU *07064213990* 23/09/2018. ASALIN RUBUTUN MUN YISHI NE TUN RANAR 18/DEC/2013).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI