ANNABI MASOYIN AL'UMMARSA (SAWW).
``` Hakika in dai zamuyi adalci, to tabbas babu wanda ya kamata muso shi, Mu bishi, mu girmamashi, Mu kambama shi, Kamar Manzon Allah (saww). Shi ya kamata Muyi soyayya don soyayyarsa, Muyi kiyayya don kiyayyarsa kamar yadda Allah yake yi. Domin babu wanda yasomu, ya damu da sha'aninmu, Kuma yake tausayinmu Kamar Annabi Muhammadu (saww). Zan kawo wasu Misalai daga cikin irin soyayyarsa da kulawarsa garemu kamar haka : 1. Lokacin da Kafirai suka matsa wajen chutar dashi da mabiyansa, an nemi alfarma agareshi cewa ko zai yi addu'a irin wacce Annabi Nouhu (as) yayi, sai yace "A'a. Ya Allah ka shiryi Mutanena. Domin su basu sanni bane". Kunga da ache yayi waccan addu'ar, da tuntuni mun hallaka. To amma da yake shi BIL MU'UMINEENA RA'UUFUN RAHEEMUN ne, sai bai yi haka ba. Yayi mana alkhairin da babu iyaka. 2. Lokacin fitar rai, kowa ya san cewar mutum ba ya iya tunawa da kowa awannan lokacin. Ta kansa yakeyi. Amma Manzon Allah (saww) bai manta damu ba.