HALAYEN MASU TSORON ALLAH (5)
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI.
Salati da aminci da girma su tabbata bisa Annabin Rahama, Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa masu haske da sahabbansa masu albarka.
Wannan shine kashi na biyar acikin darasinmu mai suna HALAYEN MASU TSORON ALLAH (SWT).
Abubakar Ibnu Abi Shaibah ya ruwaito wani hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (rta) daga Manzon Allah (saww) yana cewa :
"Ku karbi labari daga Banu Isra'eela babu makawa. Domin kuwa akwai abubuwan mamaki acikinsu".
Sannan yaci gaba da bada labari yana cewa :
"Wasu Jama'a (daga banu Isra'ila) sun fita zuwa wata makabarta, sai suka ce "Mai zai hana mu sallaci raka'a biyu sannan mu roki Allah ya fito mana da wani daga cikin Matattun nan domin ya bamu labari game da mutuwa!".
"Sai suka aikata hakan. Nan take sai ga wani mutum ya fito da kansa ta cikin wani Qabari, ga gurbin sujadah nan yana yin haske atsakiyar goshinsa.
Sai yace musu "Ya Ku wadannan! Mai kuke nufi gareni? Domin hakika Wallahi ni na rasu ne tun shekaru ɗari (100) amma har yanzu ban dena jin zafin ɗacin mutuwa ba, Don Allah ku roki Allah ya mayar dani kamar yadda nake (cikin ƙabarina)".
Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! 'yan uwa kunji mumini, mutumin kirki wanda yayi shekaru ɗari da mutuwa, amma bai dena jin raɗaɗin zafin mutuwa ba.. Kuma wannan abun yana nan tafe ga kowanne dayan cikinmu!!
Sahabin Manzon Allah (saww) mai suna Amru bn Al-Aas (rta) ya kasance yana da wani buri. Burin nasa shine ya kasance yana cewa:
"Wallahi ni kuwa zanso inga wani mutum mai zurfin hankali kuma mai yawan ibadah, adaidai lokacin da mutuwa tazo masa, domin ya bani labari game da yadda mutuwa take".
Ana nan, ana nan... Rannan sai ga Sayyiduna Amru bn Al-Aas mutuwa tazo masa. Yayin da mutanensa suka zo gareshi sai suka tuno masa da waccan maganar.
Suka ce masa "Ya Kai Baban Abdullahi, kaine ka kasance kana cewa zaka so kaga wani mutum mai zurfin hankali mai yawan himmar ibadah, yayin da mutuwa tazo masa, domin ya baka labarinta. To yanzu mu agaremu kai ne wannan mai zurfin hankalin kuma mai himmar ibadah. Kuma yanzu gashi mutuwa tazo maka. Don haka muna so ka bamu labarin yadda take.
Sai yace "HAKIKA JI NAKEYI KAMAR SAMMAI NE SUKA RUGUZO AKAN QASA, KUMA NI INA TSAKANINSU (WATO KAMAR SAMA DA QASA SUN HADU SUN MATSE NI)..
Yace "KUMA JI NAKEYI TAMKAR RAINA ANA ZARESHI NE TA CIKIN KOFAR ALLURA".
Allahu Akbar!! 'Yan uwa kunga wannan fa Sahabin Manzon Allah ne (saww) amma kunji bayani daga bakinsa akan yadda yake jin zafin radadin fitar rai!.
Acikin wata ruwaya ance Annabi Ibrahim Khalilullahi (as) watarana yace ma Mala'ikan mutuwa "Shin zaka iya nuna min da irin siffar da kake bayyana idan zaka damƙi ruhin Fajiri?".
Sai Mala'ikan mutuwan yace masa "Shin zaka iya jurewa ka kalleni awannan siffar?". Sai yace "Kwarai kuwa".
Sai Mala'ikan mutuwan ya juya baya, yayin da ya juyo ya kalli Annabi Ibraheem (as), sai Annabi Ibrahim din ya ganshi a siffar wani mutum (BAƘI WULUK) mai baƙaƙen tufafi, Mai duguzazan gashi, Mai ɗoyi, Tartsatsin wuta da wani mummunan baƙin hayaƙi yana fita ta bakinsa da hancinsa.... (LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAAH).
Nan take sai Annabi Ibrahim (as) ya faɗi ya suma... Yayin da ya farfaɗo har Mala'ikan mutuwan ya dawo ainahin siffarsa ta farko.
Sai yace masa "Ya kai Mala'ikan Mutuwa! Wallahi da ache fajirin mutum ba zai haɗu da wata azaba ba, sai dai kallon siffar fuskar nan taka, to da ya isheshi bala'i".
Bararren bawan Umar bn Khattab (rta) mai suna ASLAMU (rta) yana cewa : "Idan sauran zunubi ya saura akan mumini, kuma gashi ayyukansa ba zasu kaishi ba, to akan tsananta masa zafin mutuwa yayin da ransa yazo fita domin ta dalilin wannan zafin radadin fitar rai din ya samu kaiwa darajar matsayinsa na aljannah".
"Shi kuwa kafiri idan ma ya aikata alkhairi, akan juyar dashi cikin rangwame dan kadan da za'ayi masa wajen fitar ransa. Daga nan kuma a wuce dashi zuwa wuta".
Kunga kenan wato ashe zunubai idan suka yawaita akan mutum, to yakan janyo masa zafin radadin fitar rai. Ashe kenan babu abinda ya kamata garemu in banda mu Yawaita Istighfari da sauran nau'o'in zikirin Allah. Domin shi zikirin Allah babu abinda ya kaishi wanke zunuban bayin Allah.
Ya Allah mun tuba ka yafe mana don falalarka da rahamarka.
Salati da aminci su tabbata bisa Annabin Farko da karshe, tare da iyalan gidansa masu albarka da Sahabbansa baki daya.
Anan zamu tsaya sai a darasi na gaba. An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp 4 ranar 08-08-2016.
Comments
Post a Comment