SAMFURIN HALITTAR DAN ADAM

Acikin kowanne Jima'i guda, mafi Qarancin Kwayoyin Maniyyin da suke fita daga jikin Namiji lafiyayye sun kai kamar kimanin guda Million Arba'in (40,000,000). Wani Namijin ma yakan fitar da sama da Million dari biyu da hamsin (250,000,000).

Kowanne guda daya daga cikin wadannan Miliyoyin idan ya kyankyashe kwai za'a iya samun Mutum cikakke. To amma daga cikinsu din nan guda daya ne wanda Allah zai zaba ya samu shiga cikin Kwan halittar mace, daga nan kuma idan ya kyankyashe kwan sai su hadu su chure su zama gaurayen ruwan Maniyyi wanda shi ake kira "NUTFAH", wanda daga gareshi aka halicceka.

Imamul Lalka'eey ya fitar da hadisi tare da isnadinsa mai inganci har zuwa Kan Sahabin Manzon Allah (saww) mai suna Sayyiduna Abdullahi bn 'Amru bn Al-Aas (rta) yana cewa:

"Idan gaurayeyyen ruwan Maniyyi ya zauna acikin Mahaifar mace har tsawon kwana arba'in, Sai wani Mala'ika yazo gareta ya dauketa (ita nutfar) ya girgizata sannan ya tafi da ita zuwa ga Allah Arrahman (Mai girma da daukaka).

Sai yace "Halicceshi Ya mafi gwanintar masu Halitta". Sai Allah ya hukunta dukkan abinda yaso na lamarinsa atare da ita, sannan a mayar da ita wajen Mala'ikan.

Sai Mala'ikan yace "Ya Ubangiji wannan 'barinsa za'ayi, ko kuma cikakke ne?".

Bayan an bayyana masa amsar sai yace "Ya Ubangiji shin wannan mai tauyayyen ajali ne, ko kuwa mai cikakken ajali?". Sai a bayyana masa amsar.

Sannan sai yace "Ya Ubangiji shin guda 'daya za'ayi ko kuwa Tagwaye ne?". Sai a bayyana masa.

Sannan sai yace "Ya Ubangiji, Shin namiji za'ayi ko kuwa Mace?". Sai a bayyana masa.

Sannan sai yace "Ya Ubangiji shin 'Matsiyaci ne ('Dan wuta) ko kuwa mai arziki ne ('Dan Aljannah)?". Sai a bayyanar masa.

Sannan sai yace "Ya Ubangiji yanko masa arzikinsa". To anan za'a yanko masa arzikinsa da ajalinsa, Sannan (Mala'ikan) ya sauko dasu gaba daya.

Ina rantse muku da Ubangijin da Numfashina yake karkashin ikonsa, Mutum ba zai samu wani abin duniya ba, sai dai gwargwadon abinda aka riga aka tsaga masa din nan".

Wannan hadisin an ruwaitoshi ta hanyar Sahabbai da dama, kuma ta hanyoyi daban daban. Ga wasu nan zan kawo :

ADUBA :

- Sharhin Usoolu I'itiqadi Ahlis Sunnah na LALKA'EEY : Juzu'i na 4 shafi na 674, 675 da kuma 1236.

- Musnadu Ahmad juzu'i na uku, shafi na 397.
- Sahihul Bukhariy hadisi na 333.
- Sahihu Muslim hadisi na 2646, da kuma na 2645, 2644.
- Tafseerin Ibnu Jareer juzu'i na 9, shafi na 110, da kuma Juzu'i na 3 shafi na 170.

To 'yan uwa kowanne 'dayan cikinmu fa, Ubangiji ya zabeshi ne tun yana ruwan maniyyi atsakanin Miliyoyin irinka ya zabeka ba tare da cewa kafi wadancan sauran da komai ba.

Ya turo Mala'ika acikin Mahaifiyarka, Mala'ikan nan ya daukeka ya kaika inda sukayi zance Allah mai rahama duk ba tare da sanin Mahaifiyar taka ba, ballantana kai!!

Acikin ruwayar Abdullahi bn Mas'ud ma, Ubangiji yakan tambayi Nutfah din "YA KE NUTFAH! SHIN WANENE UBANGIJINKI?" Sai Nutfar tace "KAI NE UBANGIJINA".

Sannan Ubangiji ya rayaka acikin mahaifiyarka har ka fito duniyar nan, yana baka ci da sha da numfashi da ikon gani da ji da tunani. Duk a kyauta.

Amma wai kaine ka rasa wanda zakayi ma butulci sai Ubangijinka Allah mai Rahama wanda ya zabeka ya fifitaka!!

Yace kayi abu kaza, ka Qi yi. Yace ka bar kaza, amma ka qi bari.. Sai Shaitan Makiyinka kake ma biyayya..  (Subhanallah).

Ya Allah mun tuba ka yafe mana don falalarka da rahamarka. Ka sanyamu cikin bayinka masu yawaita godiya agareka.

Wannan nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 (06-08-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI