ANNABI MASOYIN AL'UMMARSA (SAWW).

```Hakika in dai zamuyi adalci, to tabbas babu wanda ya kamata muso shi, Mu bishi, mu girmamashi, Mu kambama shi, Kamar Manzon Allah (saww). Shi ya kamata Muyi soyayya don soyayyarsa, Muyi kiyayya don kiyayyarsa kamar yadda Allah yake yi.

Domin babu wanda yasomu, ya damu da sha'aninmu, Kuma yake tausayinmu Kamar Annabi Muhammadu (saww). Zan kawo wasu Misalai daga cikin irin soyayyarsa da kulawarsa garemu kamar haka :

1. Lokacin da Kafirai suka matsa wajen chutar dashi da mabiyansa, an nemi alfarma agareshi cewa ko zai yi addu'a irin wacce Annabi Nouhu (as) yayi, sai yace "A'a. Ya Allah ka shiryi Mutanena. Domin su basu sanni bane".

Kunga da ache yayi waccan addu'ar, da tuntuni mun hallaka. To amma da yake shi BIL MU'UMINEENA RA'UUFUN RAHEEMUN ne, sai bai yi haka ba. Yayi mana alkhairin da babu iyaka.

2. Lokacin fitar rai, kowa ya san cewar mutum ba ya iya tunawa da kowa awannan lokacin. Ta kansa yakeyi. Amma Manzon Allah (saww) bai manta damu ba.

Yana ambatonmu, yana nema mana alfarma awajen Allah, yana yin addu'a agaremu, da haka har ya koma zuwa ga Ubangijinsa mai girma da daukaka.

3. RANAR TASHI DAGA QABARI : shima lokaci ne na tashin hankali wanda mutum ba zai iya tunowa da komai ba, saboda firgicewa akan abinda ke gabansa. Amma Manzon Allah (saww) shine farkon fitowa. Yana fitowa daga Qabarinsa zai tambayi Mala'ika Jibreelu (as) : "JIBREELU INA AL'UMMA-TA?".

4. LOKACIN RABA TAKARDU : Kowa hankalinsa ya tashi. Wasu zasu karbi takardunsu da hannun dama. Wasu kuma ta hannun hagu. Wasu kuma ta kirjinsu za'a huda afito da hannayensu ta baya sannan a basu Takardun.

Anan ma Manzon Allah (saww) yana tare damu, bai barmu ba. Duk da cewa shi ba ya daga cikin wadanda zasu karbi takardu, to amma ba zai tafi ya bar al'ummarsa su wulakanta ba.

5. LOKACIN AWUN MIZANI : Shine lokacin da iyaye ke guje ma 'ya'yansu, Su ma 'ya'yan suna gudun iyayensu. Miji yana guje ma matarsa, ita ma Matar tana guje ma Mijinta. Ballantana 'yan uwan juna ko abokai awannan lokacin zasu rika tsine ma junansu (sai dai wadanda suka yi abotarsu domin Allah).

Amma Shi Manzon Allah (saww) yana zaune awajen yana kallon irin awun da za'a yiwa al'ummarsa. Har ma akwai wadanda za'a tafi dasu wuta, amma shi zai shiga tsakani. Ya hana tafiya da mutumin. Har ma zai fito da wata takarda mai dauke da wani Salatin da wannan mutumin ya ta'ba yi masa.

Idan aka dora wannan salatin akan Mizani sai ya rinjayi dukkan zunubansa. Don haka sai a tafi dashi aljannah.

6. LOKACIN HAWAN SIRADI : Shima yana daga cikin mafiya girman abubuwan tashin hankali awannan ranar. Kowanne mutum sai yazo ya hau ta kan siradi.

Wasu zasu wuce cikin sauri, wasu kuma tare da jinkiri. Wasu kuma kafin su wuce sai siradin ya kwaye naman jikinsu, yayi musu kacha kacha.

Wasu kuma zasu afka cikin ramin wutar dake Qasansa (wato cikin jahannama kenan).

To amma Manzon Allah (saww) shine farkon wucewa. Kuma ba zai gushe daga chan karshen siradin ba, har sai dukkan al'ummarsa sun wuce. Yana tsaye yana yi musu addu'a tare da Mala'ika Jibreelu (as).

7. BAYAN AN SHIGA ALJANNAH : Bayan 'yan Aljannah sun shiga Aljannah, 'yan wuta ma sun shiga wuta, to Manzon Allah (saww) ba zama zai yi ba..

Zai je ya nemi wata alfarma awajen Rabbul Izzati Wal Jalaali akan cewa yana so zai shiga cikin wutar domin yin ceto ga al'ummarsa. Domin shi ba zai iya jin dadin zama acikin gidan Aljannah alhali al'ummarsa suna cin wuta ba.

Idan aka bashi wannan alfarmar, zai je ya shiga cikinta ya fidda dukkan wanda akwai kwayar imani azuciyarsa. Komai girman laifinsa in dai ya mutu da imani a zuciyarsa to zai samu shiga cikin wannan cheton.

Saboda tsananin yalwar wannan ceton, shi kansa shaitan (L. A.) ma sai yasa rai ko zai samu shiga!! (ALLAHU AKBAR!).

8. BABBAN CETO : Wato Shafa'atul Kubra kenan. Tun farko alokacin Da halittu suka taru a filin Alqiyamah, Ubangiji yayi fushin da bai ta'ba yin irinsa ba, Don haka dukkan Annabawa da Manzanni da Mala'iku kowa ta kansa yakeyi..

Amma Manzon Allah (saww) shi kadai ne zai iya tunkarar Allah awannan ranar, ya nema ma dukkan halittu alfarma awajen Allah. Bayan dukkan manyan Manzanni anje wajensu amma sun kasa zuwa neman alfarmar.

Saboda wannan gwanintar da yayi awannan lokacin sai dukkan halittu sunyi yabonsa. Wannan shine MAQAMUL MAHMOUD wanda Ubangijinsa yayi masa alkawari (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

9. ACIKIN ALJANNAH : Su ma 'yan Aljannah bayan cewa sun shiga aljannar ne da alfarmarsa, to zai nemi wata alfarmar awajen Allah, za'ayi masa izini. Allah zai Qara ma kowannensu matsayi akan matsayin da yake dashi, da albarkar Annabi Muhammadu (saww).

Tambaya anan ita ce : Bayan imani dashi da kuma biyayya ga abinda yazo dashi, wanne abu zamuyi mu biyashi?.

Amsa ita ce : BABU. to amma Allah yace masa "KACE MUSU BA NA TAMBAYARKU WANI LADA AKANSA (WATO ABINDA NAZO MUKU DASHI) SAI DAI (KUYI) SOYAYYA GA MAKUSANTANA".

Su waye makusantansa? Sune iyalan gidansa. Kamar yadda yazo acikin hadisi.

Sayyiduna Abubakrin (rta) yana cewa "KU GIRMAMA ANNABI MUHAMMADU CIKIN LAMARIN IYALAN GIDANSA" (Wato ku girmamasu ku kyautata musu domin soyayyar da kukeyi masa).

Tabbas Annabi (saww) yayi mana soyayya da kulawa wacce ta zarce irin ta sauran Manzanni da al'ummominsu.

Ya Ubangijin dukkan komai, kayi salati da tasleemi bisa Annabinka mai Makurar daraja awajenka, gwargwadon yawan motsin dukkan masu motsi, da numfashin dukkan masu numfashi. Ka sanya iyalan gidansa da dukkan Sahabbai da mutanen kirki tare damu baki daya.

An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp - 4 aranar 16-11-1437 (19-08-2016).```

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI