A KOWANNE HALI KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA TARA :

1. Duk lokacin da wata ni'ima ta sameka, ka gode ma Allah kafin ka gode ma kowa. Kace "ALHAMDULILLAH".

2. Duk lokacin da wata musibah ta sameka, Ka zargi kanka Kar ka zargi kowa. Kuma kace "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN".

3. Duk lokacin da Qofofin samunk suka toshe, to lallai sai ka tuno da yawan zunubinka. Ka yawaita ASTAGHFIRULLAH".

4. Duk lokacin da al'amura suka rinchabe maka, ko kuma Makiya suka sawoka gaba, Komai girman abun bai fi Qarfin Allah ba.  Don haka ka yawaita "LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BIL-LAAHIL ALIYYIL 'AZEEM".

5. Duk lokacin da Bakin ciki ya dameka, ko kuma bukatunka suka toshe, to ka yawaita Salati ga fiyayyen Halittu (saww) domin salatinsa yana haskaka zuciya, yana yaye damuwa, yana kawar da bakin ciki.

6. Duk lokacin da kaji zuciyarka ta bushe ta kekashe, (Babu tsananin taushin nan na tsoron Allah) To ka yawaita karatun Alqur'ani. Domin shi karatun Alqur'ani tare da Tadabburi (zurfafa tunani) cikin Ma'anoninsa, shine fiyayyen Maganin chututtuka na fili da na boye.

7. Duk da kaje zaka aikata Sa'bon Allah, to ka tuno da cewa yana nan tare dakai. Yana jin ka, yana kallonka. Kuma akwai ranar tsayuwarka agabansa domin karbar sakamako akan dukkan ayyukanka.

8. Duk lokacin da kazo yin addu'a, to kayi ma iyayenka kafin kayi ma kanka. Duk lokacin da ka samu wadata, to ka kyautata ma iyayenka kafin ka kyautata ma kanka. Domin su ma haka suka fifita bukatunka akan nasu bukatun lokacin kana Qarami.

9. Duk lokacin da zakayi magana da Malamai ko AHLUL BAITI to ka sanya ladabi acikin furucinka. Duk da cewa kai baka riski Annabi ba, to sune magadan Annabawa (as). Wadannan su ke dauke da abinda aka aikoshi dashi. Wadannan kuma sune zuriyarsa.

Wannan nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP. Kuma muna Qara yin magiya ga barayin fasaha cewa su dubi girman Allah su dena cin amanar Ilimi. Allah yana nan a madatsa.

ZAUREN FIQHU (28-10-1437) 02-08-2016.

Comments

  1. Jazakallahu khairan Mallam. Allah ya taimake mu. Amin

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI