MAGANIN KAIKAYIN GABA
MAGANIN KAIKAYIN GABA
TAMBAYA TA 1876
********************
Ass. Mallam ya dawainiya da jamaa Allah yajikan iyaye amen.
1.Matata ce take fama da kaikayin gaba ataimaka mana da Magani.
2. Maganin karfin mazakuta saboda shekaruna basuwuce talatinba amma idan ina jimai daga naje sau daya sai innakoma a Karo nabiyu sai gabana ya mutu. Ataimaka mana da magani nagode. Daga U. Abdullah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi kaikayin gaba yana da dalilai da suke kawoshi. Idan ba'a magance ainahin dalilin ba, to gaskiya za'a dade ana shan magani amma ba za'a samu nasara sosai ba.
Idan tana da Jinnul Ashiq (Aljanin soyayya) wanda ke zuwa yana saduwa da ita, to lallai zatayi fama da Qaikayin gaba. Kuma ba ya jin magani har sai an magance ainahin aljanin dake tare da ita tukunna.
Idan kuma wata chuta ce wacce ake dauka ta hanyar Jima'i, to shima sai an maganceshi kafin Kaikayin ya dena.
- Ta nemi garin Hulba cokali 2, garin Magarya shi kuma cokali uku, garin lalle cokali biyu. Ta hadasu waje guda ta gauraya. Sannan ta rika diba tana dafawa tana zama cikin ruwan dumin.
Sannan ta nemi AL-MUMTAZ na Zauren Fiqhu ta rika yin matsi dashi. In sha Allahu zaku ga abin mamaki. Domin in sha Allahu kaikayin zai dena, kuma zata samu lafiya da ni'ima sosai.
2. Kai kuma ka nemi Man Jirjir ka rika zuba cokali guda acikin ruwan Lipton kana sha kullum bayan Sallar Isha'i. In sha Allahu zaka samu Qarfi sosai.
Amma ka hada da motsa jiki, da kuma kulawa da yana n abincin da kake ci.
WALLAHU A'ALAM.
ZAUREN FIQHU (02-03-2016).
Allah Gafarta Malam Ni Ma Ina Fama Da Kaikayin Gaba Kuma Ni Na Miji Ne Shin Xan Iya Amfani Da Wannan?
ReplyDelete