Posts

Showing posts from March, 2018

ALAMOMIN ANNABTAR DAKE JIKINSA (SAWW)

ALAMOMIN ANNABTA AJIKINSA (*SAWW) ****************************************** Allah Madaukakin Sarki ya sanya alamomin Annabta agurare goma sha biyu acikin jikin Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kamar yadda yazo acikin hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (rta) yace : 1. Akwai alama daga saman kansa. 2. Akwai alama akan goshinsa. 3. Akwai alama acikin idanunsa. 4. Akwai alama akan hancinsa mai daraja. 5. Akwai alama acikin kunnensa. 6. Akwai alama akan harshensa. 7. Akwai alama acikin yawun bakinsa. 8. Akwai alama acikin tafin hannunsa. 9. Akwai alama acikin yatsun hannayensa. 10. Akwai alama atsakanin kafadunsa. 11. Akwai alama acikin tsawon jikinsa (saww). 12. Akwai alama a sawayensa masu daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). - Amma alamar dake saman kansa ita ce kasancewarsa idan yana tafiya girgije ne ke yi masa inuwa. - Amma alamar dake kan goshinsa ita ce duk lokacin da yayi niyyar ziyartar wasu mutane  haske kan lullubesu (tun kafin zu

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (09)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (9) ******************************** Idan Qarshen duniya ya kusanto, akwai wata Wuta Gagaruma wacce zata bullo daga Udun (Wani yanki ne a Qasar Yemen) zata rika kora mutane zuwa ga Sham (Syria) wacce ita ce Qasar tashin Alqiyamah. Wutar zata fito ne daga Qarkashin Qasar Udun din sannan ta rika korar mutane zuwa ga Qasar Sham din. Wata irin wuta ce babba, mai ban mamaki. Zata rika bin mutane duk inda suka shiga. Tana kwana tare dasu, tana wuni tare dasu, tana wayar gari aduk wajen da suka wayi gari.. tana tsayawa aduk wajen da suka tsaya domin hutawa. (Kamar yadda Bukhariy ya ruwaito). Wutar zata korasu ne bisa siffofi uku : - Akwai wadanda ke kan ababen hawa tare da abincinsu. - Akwai wadanda ke biye dasu akan Raquma. - Akwai wadanda ke tafiya da Qafafunsu. Kuma duk wanda ya tsaya a baya, wutar tana cinyeshi. Yanzu haka Maluman fannin Ilimin Sanin yanayin Qasa da Duwatsu (Geologist) suna gargadi ga Mutanen dake rayuwa awannan yankin na Udun cewa su den

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (091)

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (91) SALLAR HANTSI (WALAHA) **************************** Hadithi daga Thabitu bn Ajlan daga Alqasim bn Muhammad daga Abu Umamah (rta) yace Manzon Allah (saww) yana cewa : "IDAN RANA TA FITO DAGA MAFITARTA KAMAR SIFFARTA NA LOKACIN LA'ASAR SANDA TAKE FADUWA A MAFADARTA, SAI MUTUM YA SALLACI RAKA'A BIYU DA SUJADU GUDA HUDU, TO ZA'A RUBUTA MASA LADAN WANNAN WUNIN KUMA A KANKARE MASA KUSAKURENSA DA ZUNUBANSA. KUMA IDAN YA MUTU AWANNAN RANAR ZAI SHIGA ALJANNAH". ADUBA : Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy (Juzu'i na 8 shafi na 192). QARIN BAYANI *************** Wannan lokacin da ake nufi acikin wannan hadisin shine lokacin hantsi. Domin shine ka'dai lokacin da yayi kama da lokacin faduwar rana. Hakika sallar walaha teana da lada mai yawa. Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin hadisai masu yawa. Har ma akwai hadisin dake nuna cewa duk wanda ya sallaci walaha ladansa kamar na wanda yayi sadaqah ne sau 360. Allah yasa

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (091)

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (91) SALLAR HANTSI (WALAHA) **************************** Hadithi daga Thabitu bn Ajlan daga Alqasim bn Muhammad daga Abu Umamah (rta) yace Manzon Allah (saww) yana cewa : "IDAN RANA TA FITO DAGA MAFITARTA KAMAR SIFFARTA NA LOKACIN LA'ASAR SANDA TAKE FADUWA A MAFADARTA, SAI MUTUM YA SALLACI RAKA'A BIYU DA SUJADU GUDA HUDU, TO ZA'A RUBUTA MASA LADAN WANNAN WUNIN KUMA A KANKARE MASA KUSAKURENSA DA ZUNUBANSA. KUMA IDAN YA MUTU AWANNAN RANAR ZAI SHIGA ALJANNAH". ADUBA : Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy (Juzu'i na 8 shafi na 192). QARIN BAYANI *************** Wannan lokacin da ake nufi acikin wannan hadisin shine lokacin hantsi. Domin shine ka'dai lokacin da yayi kama da lokacin faduwar rana. Hakika sallar walaha teana da lada mai yawa. Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin hadisai masu yawa. Har ma akwai hadisin dake nuna cewa duk wanda ya sallaci walaha ladansa kamar na wanda yayi sadaqah ne sau 360. Allah yasa

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (06)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (06) ********************************* Saboda tsananin girman Sha'anita, Ubangiji ya kirata da sunaye kala-kala daban-daban, domin ya nuna ma bayinsa su gane Muhimmancinta, don su nemi guzurin zuwanta. Allah ya kirata da suna : - Mai Qwankwasar Zukata, saboda yadda faduwar gaba ke afkuwa ga halittu awannan ranar. - RANAR GASKIYA : Allah ya kirata da wannan sunan ne domin babu wanda ya isa ya furta Qarya awannan ranar. Domin kuwa Allah yana toshe bakin kafirai da munafukai, Kuma zai yi magana ne da gabobin jikinsu wadanda dasu ne aka je aka aikata laifin da ake tuhumarsu akai. - RANAR RARRABEWA : Allah ya kirata da wannan sunan ne domin awannan ranar ne za'a rarrabe tsakanin 'Yan Wuta da 'Yan Aljannah.. Ita ce ranar da azzalumai zasu rika cizon yatsa akan 'barnar da suka riga suka yiwa kansu na sa'bon Allah da kuma yin jayayya da Manzannin Allah (alaihimus salam). Allah ma yayi rantsuwa da ita ne domin ya nuna mana tabbatar afkuwar

RANAR DA ZAKA YI EXPIRE

RANAR DA ZAKAYI EXPIRE **************************** Ya kai 'Dan Adam!! Ya kai wanda duniya take zugashi tana rudinsa!! Ya kai wanda dogon buri ya cika zuciyarka!!! - Anya kana tuna ranar da zakayi expire kuwa? Wato ranar da zaka tashi daga aiki... Ranar da zaka bar duniya tare dukkan abinda ka mallaka.. - Kamar yadda Kowanne kayan kampani yake da expiry date ajikinsa, hakanan kaima kana da taka ranar tana nan arubuce awajen Ubangijinka. - Watakil idan ta kusanto ya bayyana maka alamun zuwanta. Watakil kuma sai dai ta riskeki "Baghtatan" ba tare da wani kintsi ba!!. - Kamar yadda mutane suke kyamar dukkan abinda yayi expire, to hakanan daga wannan ranar bayan sun binneka, iyalanka zasu kyamaceka. Babu wanda zai yarda ya tayaka kwanciya acikin Qabarinka. Koda shi yana daga waje, kai kana ciki... Ba zai yarda ba. - Wani ma tun daga addu'ar da yayi maka aranar, to ba zai Qara zama don yin addu'a agareka ba. Ba zai so yaji ambatonka ba. - Da zarar sun dawo dag

MAI DA'DIN SUNAYE (09)

Da Sunan Allah Gwani Mai Hikimar da bata Misaltuwa, Mai Rahamar da bata Qidayuwa, wanda cikin Gwanintarsa ya halicci Jinsin Mutum kuma ya fifitashi sama da mafiya yawan halittunsa. Salati maras farko da Qarshe ya tabbata bisa Annabin da Allah ya aikoshi domin rahama da Jin Qai ga dukkan halittu.. Tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Ma'abota bin tafarkin gaskiya. Acikin darasinmu na sharhin sunayen Ma'aikin  Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yau in sha Allahu zamu tashi ne daga kan suna na goma sha biyar (15) wato : 15) BASHEERUN NADHEERUN : Wato Mai bishara ga dukkan muminai kuma mai gargadi ga dukkan duniya. Shine Annabin da Allah ya aiko zuwa ga dukkan duniya baki daya domin ya zama mai bishara kuma mai gargadi garesu. Yayi bishara ga muminai cewa lallai duk wanda yayi imani kuma ya aikata ayyuka na kwarai to sakamakonsa shine Aljannatai wadanda Qoramu ke gudana ta karkashinsu. Kuma zasu samu dukkan abinda suk