ALAMOMIN ANNABTAR DAKE JIKINSA (SAWW)

ALAMOMIN ANNABTA AJIKINSA (*SAWW)
******************************************
Allah Madaukakin Sarki ya sanya alamomin Annabta agurare goma sha biyu acikin jikin Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kamar yadda yazo acikin hadisin Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (rta) yace :

1. Akwai alama daga saman kansa.

2. Akwai alama akan goshinsa.

3. Akwai alama acikin idanunsa.

4. Akwai alama akan hancinsa mai daraja.

5. Akwai alama acikin kunnensa.

6. Akwai alama akan harshensa.

7. Akwai alama acikin yawun bakinsa.

8. Akwai alama acikin tafin hannunsa.

9. Akwai alama acikin yatsun hannayensa.

10. Akwai alama atsakanin kafadunsa.

11. Akwai alama acikin tsawon jikinsa (saww).

12. Akwai alama a sawayensa masu daraja (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

- Amma alamar dake saman kansa ita ce kasancewarsa idan yana tafiya girgije ne ke yi masa inuwa.

- Amma alamar dake kan goshinsa ita ce duk lokacin da yayi niyyar ziyartar wasu mutane  haske kan lullubesu (tun kafin zuwansa).

- Amma alamar dake cikin Idanuwansa ita ce kasancewarsa yana kallon na bayansa kamar yadda yake kallon na gabansa.

- Ya kasance yana jin Qamshi amma ba ya jin Wari.

- Amma alamar dake cikin kunnuwansa ita ce kasancewarsa yana jin Qarar Alqalamin allon Lauhul Mahfooz.

- Amma alamar dake kan harshensa ita ce kasancewarsa ba ya fa'dar abu sai gaskiya. Kuma ba ya yin furuci sai na gaskiya.

- Amma alamar dake cikin yawun bakinsa ita ce kasancewarsa idan ya tofa yawunsa acikin ruwan zartsi, sai ya koma ya zama ruwan da'di.

- Amma alamar dake kan tafin hannunsa ita ce kasancewarsa idan ya debi tsakuwa takan yi tasbeehi akan tafin hannunsa.

- Amma alamar dake tsakanin kafadunsa ita ce Khatimin Annabtar dake kusa da kafadarsa ta haggu. Rubutu ne layi biyu da aka yisu da haske.

-.Amma alamar dake tare da tsawonsa shine kasancewarsa idan ya jera da dogon mutum sai ya zarceshi tsawo. Idan kuma ya jera da madaidaicin mutum sai yayi daidai dashi.

- Amma alamar dake tare da sawayensa ita ce kasancewarsa idan yana tafiya akan yashi ko rairayi ba'a ganin wajen da ya taka. Amma idan yana tafiya akan duwatsu  sai alamar tafin sawunsa ya bayyana.

Ya Allah kayi salati da aminci da albarkoki da rahama madawwama bisa Shugabanmu macecinmu abin Qaunarmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Salihan bayinka.. Adadin dukkan halittun ruwa da tudu, da adadin halittun sammai da Qassai.. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (02-07-1439 19/03/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI