HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (091)

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (91)

SALLAR HANTSI (WALAHA)
****************************
Hadithi daga Thabitu bn Ajlan daga Alqasim bn Muhammad daga Abu Umamah (rta) yace Manzon Allah (saww) yana cewa :

"IDAN RANA TA FITO DAGA MAFITARTA KAMAR SIFFARTA NA LOKACIN LA'ASAR SANDA TAKE FADUWA A MAFADARTA, SAI MUTUM YA SALLACI RAKA'A BIYU DA SUJADU GUDA HUDU, TO ZA'A RUBUTA MASA LADAN WANNAN WUNIN KUMA A KANKARE MASA KUSAKURENSA DA ZUNUBANSA. KUMA IDAN YA MUTU AWANNAN RANAR ZAI SHIGA ALJANNAH".

ADUBA :

Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy (Juzu'i na 8 shafi na 192).

QARIN BAYANI
***************
Wannan lokacin da ake nufi acikin wannan hadisin shine lokacin hantsi. Domin shine ka'dai lokacin da yayi kama da lokacin faduwar rana.

Hakika sallar walaha teana da lada mai yawa. Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin hadisai masu yawa.

Har ma akwai hadisin dake nuna cewa duk wanda ya sallaci walaha ladansa kamar na wanda yayi sadaqah ne sau 360.

Allah yasa mu dace da samun wannan babbar falala. Ameen. Zaka iya yinta kafin ka tafi wajen aiki ko kasuwarka. Tun daga karfe 7:30 har zuwa 11:45 duk lokacin Walaha ne. Hasali ma lokacinnata yafi haka fa'di.

Allah yasa mu dace ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (27/02/2018  11/06/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI