IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (06)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (06)
*********************************
Saboda tsananin girman Sha'anita, Ubangiji ya kirata da sunaye kala-kala daban-daban, domin ya nuna ma bayinsa su gane Muhimmancinta, don su nemi guzurin zuwanta.

Allah ya kirata da suna :

- Mai Qwankwasar Zukata, saboda yadda faduwar gaba ke afkuwa ga halittu awannan ranar.

- RANAR GASKIYA : Allah ya kirata da wannan sunan ne domin babu wanda ya isa ya furta Qarya awannan ranar. Domin kuwa Allah yana toshe bakin kafirai da munafukai, Kuma zai yi magana ne da gabobin jikinsu wadanda dasu ne aka je aka aikata laifin da ake tuhumarsu akai.

- RANAR RARRABEWA : Allah ya kirata da wannan sunan ne domin awannan ranar ne za'a rarrabe tsakanin 'Yan Wuta da 'Yan Aljannah..

Ita ce ranar da azzalumai zasu rika cizon yatsa akan 'barnar da suka riga suka yiwa kansu na sa'bon Allah da kuma yin jayayya da Manzannin Allah (alaihimus salam).

Allah ma yayi rantsuwa da ita ne domin ya nuna mana tabbatar afkuwarta.

Yace : “BA SAI NAYI RANTSUWA DA RANAR TSAIWA BA!”

Kuma Ubangiji yayi rantsuwa game da afkuwarta a inda yake cewa :

"HAKIKA ALQIYAMAH LALLAI MAI ZUWA CE BABU KOKWANTO CIKINTA".

Kuma ya bada labarinta kamar ma har ta riga tazo. A inda yake cewa : "AL'AMARIN ALLAH (WATO ALQIYAMAH) YA RIGA YAZO".

Allah bai gushe ba yana kusanto mana da labarinta har sai da ya nuna mana kamar gobe-gobe zata afku.. Inda yake cewa :

"LALLAI KOWACCE RAI TA DUBA ABINDA YA GABATAR SABODA GOBE (WATO ALQIYAMAH).

Hakika Alqiyamah lamarinta da grima yake.. Rana ce wacce dukkan halittu zasu taru waje guda domin karbar sakamakon abinda suka gabatar na ayyukansu. Akwai babban tashin hankali game da wannan ranar wanda ke sanya jariri ya fidda furfura!!!.

Ubangiji ya bada labari game da bayinsa muminai cewa "MASU TSORO NE DAGA GARETA, KUMA SUN SAN CEWA ITA (ALQIYAMAH DIN) GASKIYA CE".

Don haka Muminai suke yin tanadi saboda zuwanta. Suna tsarkake ayyukansu suna gyara zukatansu, kuma suna tashi tsaye wajen neman guzuri domin zuwanta.

To tambaya anan ita ce :

Wanda bai san komai game da tashin hankalinta ba, bai san siffofinta ba, bai san komai game da wahalhalun dake afkuwa acikinta ba, to ta yaya zai rika tunawa da ita, balle yayi tanadi domin zuwanta, har ma zuciyarsa ta rika kaduwa saboda tsananin tunanin zuwanta??

Shi yasa Zauren Fiqhu ya Quduri aniyar ci gaba da kawo wadannan Maqaloli da rubuce-rubucen domin Qara ma juna sani, da kuma Qara ma juna himma game da neman guzurin wannan babban lamari.

Ya Allah kasa mu cika da imani, Ka kyautata Qarshenmu ka sanyamu cikin bayinka wadanda zaka shigar dasu Aljannah Firdausi ba tare da hisabi ko Uqubah ba. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 09094623006 (11-06-1439 27-02-2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI