IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (09)

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (9)
********************************
Idan Qarshen duniya ya kusanto, akwai wata Wuta Gagaruma wacce zata bullo daga Udun (Wani yanki ne a Qasar Yemen) zata rika kora mutane zuwa ga Sham (Syria) wacce ita ce Qasar tashin Alqiyamah.

Wutar zata fito ne daga Qarkashin Qasar Udun din sannan ta rika korar mutane zuwa ga Qasar Sham din.

Wata irin wuta ce babba, mai ban mamaki. Zata rika bin mutane duk inda suka shiga. Tana kwana tare dasu, tana wuni tare dasu, tana wayar gari aduk wajen da suka wayi gari.. tana tsayawa aduk wajen da suka tsaya domin hutawa. (Kamar yadda Bukhariy ya ruwaito).

Wutar zata korasu ne bisa siffofi uku :

- Akwai wadanda ke kan ababen hawa tare da abincinsu.

- Akwai wadanda ke biye dasu akan Raquma.

- Akwai wadanda ke tafiya da Qafafunsu.

Kuma duk wanda ya tsaya a baya, wutar tana cinyeshi.

Yanzu haka Maluman fannin Ilimin Sanin yanayin Qasa da Duwatsu (Geologist) suna gargadi ga Mutanen dake rayuwa awannan yankin na Udun cewa su dena tashin wuta a dazuzzuka. Domin kuwa su masanan sun gano cewar akwai wata Wuta dake ci a chan Qasan Qarkashin Qasar wannan yankin. Wacce kuma zata iya bayyana adoron Qasa a kowanne lokaci.

Wannan taron jama'ar da za'ayi a Qasar Sham shine taro na biyu irinsa anan rayuwar duniya. Amma a lahira ma akwai sauran taruka irin wannan har guda biyu :

- Taron hisabi : Wanda dukkan halittu ne zasu tsaya domin awun mizani da karbar sakamakon ayyukansu.. Har zuwa tsawon dadewar gwargwadon yadda Allah yaso..

- Taruwar Muminai Zalla kafin shiga Aljannah.. Dukkan Muminai na kowacce al'ummah zasu taru domin shiga Aljannah. Amma Qofofinta suna kulle har sai Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yazo ya kwankwasa an bude masa ya shiga sannan kowa ma ya samu shiga.

Wannan wutar tana daga cikin manyan alamomin tashin Alqiyamah. Kuma a bayanta ne Allah zai tashi Alqiyamar. Sai dai babu wani wanda yasan ainahin lokacinta koda cikin Annabawa da Manzanni da Mala'iku (alaihimus salam). Allah ne ya kebanci kansa da wannan sanin, kamar yadda Alqur'ani ya bayyana.

Hakika lallai Lamarin Alqiyamah da girma yake!! Tashin hankalinta da yawa yake.. Lokacinta kusantowa yake!! Razaninta kullum hauhawa yake!!..

Ya Allah kasa mu cika da imani Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU (22-03-2018 05/07/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI