MAI DA'DIN SUNAYE (09)
Da Sunan Allah Gwani Mai Hikimar da bata Misaltuwa, Mai Rahamar da bata Qidayuwa, wanda cikin Gwanintarsa ya halicci Jinsin Mutum kuma ya fifitashi sama da mafiya yawan halittunsa.
Salati maras farko da Qarshe ya tabbata bisa Annabin da Allah ya aikoshi domin rahama da Jin Qai ga dukkan halittu.. Tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa taurarin shiriya, da dukkan Ma'abota bin tafarkin gaskiya.
Acikin darasinmu na sharhin sunayen Ma'aikin Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yau in sha Allahu zamu tashi ne daga kan suna na goma sha biyar (15) wato :
15) BASHEERUN NADHEERUN : Wato Mai bishara ga dukkan muminai kuma mai gargadi ga dukkan duniya.
Shine Annabin da Allah ya aiko zuwa ga dukkan duniya baki daya domin ya zama mai bishara kuma mai gargadi garesu. Yayi bishara ga muminai cewa lallai duk wanda yayi imani kuma ya aikata ayyuka na kwarai to sakamakonsa shine Aljannatai wadanda Qoramu ke gudana ta karkashinsu. Kuma zasu samu dukkan abinda suke kwadayi ko marmari har ma abinda idanu bai ta'ba gani ba, kunne bai ta'ba jin labari ba, awajen Ubangiji Allah.
Hakanan acikin gargadin da yayi ma duniya ya gaya musu cewa Hakika duk wanda ya kafirce kuma yayi zalunci to sakamakonsa shine samun mummunar makoma awajen Allah. Wato Wuta wacce Makamashinta sune mutane da duwatsu.
Hakika mun shaida cewa Annabi Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya isar da Sakon Allah, yayi ma al'ummah nasiha, Kuma yayi jihadi ta kowacce fuska domin daukaka kalmar Allah. Kuma muna rokon Allah ya saka masa da mafi girman sakamakon da yake yiwa Manzanni akan al'ummatansu.
16. ABDULLAH (CIKAKKEN BAWAN ALLAH) : Hakika Allah Madaukakin Sarki ya kebanci Annabinsa Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da wannan sunan domin tsantsar girmamawa gareshi. Ya ambaceshi da wannan sunan a wurare masu yawa acikin littafinsa.
Misali acikin suratul jinni ayah ta 20 Allah yace : "HAKIKA YAYIN DA BAWAN NAN NA ALLAH YA TSAYA (ACIKIN SALLAH) ".
Da kuma suratul Furqan ayah ta 1, Allah yace : "ALBARKA TA TABBATA GA WANNAN DA YA SAUKAR DA ALQUR'ANI GA BAWANSA DOMIN YA ZAMTO MAI YIN GARGADI GA (DUKKAN) TALIKAI".
Acikin Suratun Najmi ayah ta 10 Allah yace : "SAI YAYI WAHAYIN ABINDA YAYI WAHAYI ZUWA GA BAWANSA".
Acikin suratul isra'i ayah ta 1 Allah yace "TSARKI YA TABBATA GA WANDA YA TAFIYAR DA BAWANSA CIKIN DARE DAGA MASALLACIN HARAMI ZUWA GA MASALLACI MAFI NISA (QUDUS)...".
Hakika dukkan talikai ma bayin Allah ne. Amma cikakken bawan Allah wanda ya cika matsayinsa na bauta (Ubudiyyah) shine Annabi Muhammadu (saww).
Yazo duniya alokacin da babu sauran goshin dake yiwa Allah sujadah adoron Qasa.. Amma ta dalilinsa gashi yanzu duniyar cike take da bayi muminai.
Shine farkon wanda ya bauta ma Allah, kuma aranar Alqiyamah ma shine ka'dai zai ma Allah bauta.. Sanda zai je yayi sujadah yayi ma kirari irin na yabo da girmamawa wanda dukkan halittu basu sanshi ba.
Ya Allah yi salati da aminci da albarkoki gareshi da iyalan gidansa masu albarka Gwargwadon matsayinsa agunka..
Ka Qara daukaka ambatonsa kamar yadda ya daukaka ambatonka. Ka cika masa burinsa ka tasheshi bisa Matsayin babban abin yabo aranar da dukkan halittu suke zargin kawunansu.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 09094623006 (03-03-2018 16-06-1439).
Comments
Post a Comment