Posts

Showing posts from October, 2018

FA'IDODIN DAKE CIKIN YIN AURE :

Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan daga ciki zamu lissafo kamar haka: 1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). 2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (saww) farin ciki aranar lahira. Yace : "Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni zanyi ma sauran al'ummomi alfahari daku aranar Alkiyamah". 3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI. 4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi maka addu'a bayan rasuwarka.  Wannan yana daga cikin ayyukan da  ladansu ba zai yanke ba har abada. 5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare masa al'aurarsa daga Zina. 6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma 'Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta kenan daga Zina. 7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da ninkawar lad

MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 1

NASABARSA : ************** Shine Shugabanmu Muhammadu 'dan Abdullahi 'dan Abdul Muttalibi 'dan Hashim 'dan Abdu Manafi 'dan Qusayyu 'dan Kilabu 'dan Murratu 'dan Ka'abu 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu 'dan Fihru 'dan Maliku 'dan Nadhru 'dan Kinanatu 'dan Khuzaimah 'dan Mudrikah 'dan Ilyas 'dan Mudhar 'dan Nizaar 'dan Ma'addu 'dan 'Adnan shi kuma Adnan yana daga cikin jikokin Annabi Isma'il (as) shi kuma 'dan Annabi Ibraheem (as). Nasabah ce tsarkakakkiya wacce babu wani datti ko Qazanta irin ta zamanin jahiliyyah da ta ta'ba ratsata. Kowanne daga cikin iyayensa da kakanninsa tsarkakakke ne kuma mafi nagartar mutanen zamaninsa. Haka kuma iyayensa mata dukkaninsu tsarkaka ne madaukaka acikin jama'ar zamunnansu. Shi da kansa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace " NI ZA'BABBE NE DAGA CIKIN ZABABBU DAGA CIKIN ZABABBU ". Allah ya zabi zuriyar gidan

MAGANIN NAKUDA DA YAWANCIN CUTUKAN MATA

Daga cikin mafiya girman fa'idodi game da maganin nakuda, asamu: 1. HABBATUS SAUDA COKALI 1. 2. ALBABUNAJ COKALI 1. Adafasu da ruwa kofi guda. idan sun tafasa asauke atace asanya zuma gwargwadon yadda ake so sannan asha da duminsa. Idan mace tana shan wannan zata samu saukin laulayin ciki. kuma idan tazo haihuwa ma abin zaizo da sauki Bi-iznillahi. Hakanan Idan aka samu Man Habbatus Sauda Mai kyau (Made in Saudi, ko Pakistan, ko Sudan ko egypt) tare da Man Albabunaj (Chamomile Oil) ahadasu arika sanya cokali guda acikin Shayi (Tea) ko Ruwan dumi, Idan mace tana sha zata samu sauki daga yawancin cututtukan da mata suke fama dashi kamar: * Kaikayin gaba * Fitar farin ruwa. * Rikicin jinin al'ada. * Matsanancin Ciwon Mara. * Namijin dare. * Ciwon ciki. * Qarancin barci. * Daukewar sha'awa. * Rashin ruwan nono. Idan matayen aure da 'Yan mata suka riki irin wadannan magungunan na Islama sun ishesu ba sai sunje suna jele a asibiti ba. Domin zuwan mace ta bude

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH 112)

HALARTAR JANA'IZA ********************** Hadisi daga Khalid bn Ma'adan daga Sayyiduna Abu Umamah (radhiyallahu anhu) cewa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "DUK WANDA YA SALLACI SALLAR JUMA'AH, KUMA YA AZUMCI WUNINTA, KUMA YA DUBA MARAR LAFIYA, KUMA YA HALARCI JANAZAH, KUMA YA HALARCI DAURIN AURE, ALJANNAH TA WAJABTA GARESHI". ADUBA MU'UJAMUL AUSAT (Juzu'i na 3 shafi na 23). Allah yasa mu dace da samun rahamarsa da falalarsa da rangwamensa ameen. Hakika dukkan wadannan abubuwan da aka lissafa, mafiya yawansu ayyuka ne dake Qara dankon zumunci da Qaunar juna atsakanin al'ummah. Kuma yinsu yana sanya farin ciki a zuciyar mumini kuma yana janyo samun yardar Allah Mai rahama. Ya Allah ka datar damu duniya da lahira. Ka bamu yardarka don falalarka da rahamarka da soyayyar da kake yiwa bayinka. Salati da aminci da albarka da martabobi su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Saliha

JARUMTAKAR SAHABBAI (02)

LABARIN WANI UBA DA 'DANSA (RA) Aranar da za'a fita zuwa yaqin badar, lokacin da Annabi (saww) ya sanar da Sahabbai cewa duk wanda yake da iko ya fito a tafi, wani baqon al'amari mai ban mamaki ya faru tsakanin Wani Sahabi mai suna Sa'adu bn Khaythamah da mahaifinsa Khaythamah bn Harith (Allah ya yarda dasu). Yayin da sanarwar fita yaqin tazo kunnensu sai Khaithamah din ya kira 'dansa yace masa "Ya kai 'dana! Hakika ayau din nan sai 'dayan cikinmu ya fita, 'daya kuma ya zauna a gida ya kula da Mata da Qananan yara. Don haka ni zan fita (zuwa badar din) kai kuma ka zauna agida ka kula da Mata da Qananan yara". Sai Sa'adu yace "Ya Babana! Wallahi wannan ba zai yiwu ba. Domin ni nafi ka kwadayin fita yaqin, Kai kuma kafi ni bukatuwa zuwa ga zaman gida. Don haka ni zan fita kai kuma ka zauna agida". Sai Baban yace "Ya kai Sa'adu sa'ba mun zakayi?  Wato ba zaka bi umurnina ba!!". Sai Sa'adu yace "Hakika

MAI TACECCEN FARI (SAWW)

Ya Allah kayi salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu Mai taceccen farin fatar jiki, ma'abocin yalwatattun idanuwa masu kyawu da kwarjini da hasken fuska,   Mai mutukar farin cikin idanu da baqin kwayar cikinsa tare da ratsina ja wanda ke nuna alamar Qarfin jiki da zuciya tare da jarumtakarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin yalwataccen gashin kai, gashin nasa baqi ne mai sheqi kuma yayi liflif akan kafadunsa. Mai yalwataccen goshi tare sissiran karan hanci, da mayalwacin gashin gira masu kyawu da kwarjini. Mai fararen hakora jerarru,  ga wushirya mai fidda haske da Qamshi yayin da yake magana. Kwarjini ya lullube murmushinsa, ga tawadhu'unsa ya mamaye dukkan lamarinsa (saww). Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin Manyan damatsu mai zara-zaran yatsu,  mai yalwar tafin hannu bisa ma'ana da zahiri. Mai Madaidaicin ciki ne shi tare da yalwar Qirji. Cikinsa da Qirjinsa sun daidaita da juna, kuma akwai wani jerarr

KU DUBI IRIN WANNAN SOYAYYA!!

Bayan an dawo daga Yakin Uhudu, kasancewar shine Yaqi na farko wanda Musulmai da yawa sukayi shahadah, Sai garin Madeena ya cika da kururuwar Mata da Qananan yara. Yayin da Manzon Allah (saww) yaji wasu mata daga dangin Banu Abdil-Ash'hal suna ta rusa kuka saboda mamatansu, Sai hankalinsa ya tashi. Ya tuna da Baffansa wato Sayyiduna Hamzah bn Abdil Muttalib (rta). Sai yace: "SAI DAI KUMA SHI HAMZA BASHI DA MASU YI MASA KUKA". Daga jin wannan Qaulin sai gaba daya Matayen mutanen Madeenah suka taho suka zauna suka fara rusa kuka domjn su taya Manzon Allah (saww) bakin cikin rabuwa da Baffansa. Suna ta kuka cikin dare har Manzon Allah (saww) yayi barci. Yayin da ya farka yaji har yanzu suna tayi, sai yace: "Ya Kaitonsu, har yanzu suna zaune anan? Ku umurcesu su koma (gidajensu) Kuma bayan wannan ranar kar su sake yin kuka bisa wani Mamaci". ADUBA : - ÃLUL BAITI HAULAR RASOOL (shafi na 101). - SUNANU IBNI MAAJAH (hadisi na 1591). Zauren Fiqhu, wannan yana n