HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH 112)

HALARTAR JANA'IZA
**********************
Hadisi daga Khalid bn Ma'adan daga Sayyiduna Abu Umamah (radhiyallahu anhu) cewa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :

"DUK WANDA YA SALLACI SALLAR JUMA'AH, KUMA YA AZUMCI WUNINTA, KUMA YA DUBA MARAR LAFIYA, KUMA YA HALARCI JANAZAH, KUMA YA HALARCI DAURIN AURE, ALJANNAH TA WAJABTA GARESHI".

ADUBA MU'UJAMUL AUSAT (Juzu'i na 3 shafi na 23).

Allah yasa mu dace da samun rahamarsa da falalarsa da rangwamensa ameen.

Hakika dukkan wadannan abubuwan da aka lissafa, mafiya yawansu ayyuka ne dake Qara dankon zumunci da Qaunar juna atsakanin al'ummah. Kuma yinsu yana sanya farin ciki a zuciyar mumini kuma yana janyo samun yardar Allah Mai rahama.

Ya Allah ka datar damu duniya da lahira. Ka bamu yardarka don falalarka da rahamarka da soyayyar da kake yiwa bayinka.

Salati da aminci da albarka da martabobi su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Salihan bayin Allah baki dayansu. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/10/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI