MAI TACECCEN FARI (SAWW)
Ya Allah kayi salati bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu Mai taceccen farin fatar jiki, ma'abocin yalwatattun idanuwa masu kyawu da kwarjini da hasken fuska, Mai mutukar farin cikin idanu da baqin kwayar cikinsa tare da ratsina ja wanda ke nuna alamar Qarfin jiki da zuciya tare da jarumtakarsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin yalwataccen gashin kai, gashin nasa baqi ne mai sheqi kuma yayi liflif akan kafadunsa. Mai yalwataccen goshi tare sissiran karan hanci, da mayalwacin gashin gira masu kyawu da kwarjini.
Mai fararen hakora jerarru, ga wushirya mai fidda haske da Qamshi yayin da yake magana. Kwarjini ya lullube murmushinsa, ga tawadhu'unsa ya mamaye dukkan lamarinsa (saww).
Kayi salati da tasleemi gareshi Ma'abocin Manyan damatsu mai zara-zaran yatsu, mai yalwar tafin hannu bisa ma'ana da zahiri. Mai Madaidaicin ciki ne shi tare da yalwar Qirji. Cikinsa da Qirjinsa sun daidaita da juna, kuma akwai wani jerarren baqin gashi wanda ya taho daga Qirjinsa zuwa cibiyarsa (saww).
Ya Allah yi salati da tasleemi gareshi gwargwadon matsayinsa awajenka, sau adadin gudanuwar lamarinka da zartuwar Qudurarka bisa dukkan halittunka..
Ya Allah ka sanya wannan salatin ya zama silar shakuwar ruhinmu da ambatonsa, kuma ya zamo silar nutsewar zukatanmu acikin kogin sonsa, da tausuwar gabobinmu cikin biyayya gareshi.
Ya Allah ka sanya tunanin wannan Annabin da ambatonsa ya zamanto abincin ruhinmu da nutsuwarmu ta zahiri da buya, ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (14/10/2018)
Comments
Post a Comment