MAGANIN NAKUDA DA YAWANCIN CUTUKAN MATA

Daga cikin mafiya girman fa'idodi game da maganin nakuda, asamu:

1. HABBATUS SAUDA COKALI 1.
2. ALBABUNAJ COKALI 1.

Adafasu da ruwa kofi guda. idan sun tafasa asauke atace asanya zuma gwargwadon yadda ake so sannan asha da duminsa.

Idan mace tana shan wannan zata samu saukin laulayin ciki. kuma idan tazo haihuwa ma abin zaizo da sauki Bi-iznillahi.

Hakanan Idan aka samu Man Habbatus Sauda Mai kyau (Made in Saudi, ko Pakistan, ko Sudan ko egypt) tare da Man Albabunaj (Chamomile Oil) ahadasu arika sanya cokali guda acikin Shayi (Tea) ko Ruwan dumi, Idan mace tana sha zata samu sauki daga yawancin cututtukan da mata suke fama dashi kamar:

* Kaikayin gaba
* Fitar farin ruwa.
* Rikicin jinin al'ada.
* Matsanancin Ciwon Mara.
* Namijin dare.
* Ciwon ciki.
* Qarancin barci.
* Daukewar sha'awa.
* Rashin ruwan nono.

Idan matayen aure da 'Yan mata suka riki irin wadannan magungunan na Islama sun ishesu ba sai sunje suna jele a asibiti ba.

Domin zuwan mace ta bude jikinta agaban likita namiji haramun ne. Sai dai in da larura wacce babu yadda za'ayi.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (Modified on 23/10/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI