JARUMTAKAR SAHABBAI (02)

LABARIN WANI UBA DA 'DANSA (RA)

Aranar da za'a fita zuwa yaqin badar, lokacin da Annabi (saww) ya sanar da Sahabbai cewa duk wanda yake da iko ya fito a tafi, wani baqon al'amari mai ban mamaki ya faru tsakanin Wani Sahabi mai suna Sa'adu bn Khaythamah da mahaifinsa Khaythamah bn Harith (Allah ya yarda dasu).

Yayin da sanarwar fita yaqin tazo kunnensu sai Khaithamah din ya kira 'dansa yace masa "Ya kai 'dana! Hakika ayau din nan sai 'dayan cikinmu ya fita, 'daya kuma ya zauna a gida ya kula da Mata da Qananan yara. Don haka ni zan fita (zuwa badar din) kai kuma ka zauna agida ka kula da Mata da Qananan yara".

Sai Sa'adu yace "Ya Babana! Wallahi wannan ba zai yiwu ba. Domin ni nafi ka kwadayin fita yaqin, Kai kuma kafi ni bukatuwa zuwa ga zaman gida. Don haka ni zan fita kai kuma ka zauna agida".

Sai Baban yace "Ya kai Sa'adu sa'ba mun zakayi?  Wato ba zaka bi umurnina ba!!".

Sai Sa'adu yace "Hakika Allah ya riga ya wajabta mun fita Jihadi kuma ga Manzonsa nan (saww) yayi kirana. Shin kana so inyi maka biyayya kuma in sa'ba wa Allah da Manzonsa kenan?".

Sai Baban yace "Ya kai 'dana! Tunda dai babu makawa sai 'dayan cikinmu na fita, to ina so kayi hakuri ka barni ni inje".

Sai 'dan yace "Ya babana!   Da ache ba Aljannah ce take kiranmu ba, da na kyaleka kaje ni in zauna din".

Khaysamah  (shi Mahaifin kenan) bai yarda ba har sai da sukayi Quri'ah atsakaninsa da 'dan nasa, Sai 'dan yaci Quri'ar kuma ya fita zuwa Yaqin Badar.

Yayi yaqi sosai har sai da yayi shahadah a badar din. To yayin da  Babansa ya samu labarin mutuwarsa yayi bakin ciki mai tsanani. Ba wai baqin cikin rabuwa da 'dansa ba. A'a bakin ciki ne bisa kansa. Cewa inama shine ya fita yayi shahadar nan!!. ALLAHU AKBAR !!!.

Yayin da ranar yaqin uhudu tazo, Khaythamah (radhiyallahu anhu) ya fito da shirin tafiya yaqin sai Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) bai bashi dama ba. (Watakil ko saboda tsufa ko kuma wani dalilin mai karfi).

Nan take sai ya fashe da kuka! Yace "Ya Rasulallahi hakika ban samu fita Yaqin badar ba,  duk da cewa nayi kwadayin hakan. Saboda tsananin kwadayin fitan har sai da mukayi Quri'ah atsakanina da 'dana. Shi yaci Quri'ar ya fita kuma Allah ya azurtashi da samun shahadah. ..

To hakika a daren yau na ganshi acikin mafarkina yana ce mun "Taho garemu ka riskemu ka zama abokin tafiyarmu acikin Aljannah. Domin hakika mun samu duk abinda Ubangijinmu yayi mana alkawari cewa gaskiya ne".

To wallahi Ya Ma'aikin Allah hakika yau na wayi gari ina jin shauqin riskuwa dashi. Duk da cewa hakika shekaruna sun yawaita, kuma qashin jikina yayi rauni. Amma ina mutukar son gamuwa da Ubangijina".

To daga jin wannan sai Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya bashi damar fita wajen Yaqin Uhudu. Yaje ya nuna jarumtakarsa sosai. Yayi yaqi har sai da yayi shahadah. Qaton Kafirin nan mai suna Amru bn Abdu wuddin ne ya kasheshi. Shi kuma Sayyiduna Aliyu (Karramal Lahu Wajhahu)  ya kashe wannan kafirin aranar yaqin Khandaq (yaqin gwalalo).

Allahu Akbar!! 'Yan uwa kunji fa irin halayen Sahabban Shugaba (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) wadanda suka fifita mutuwa afagen daukaka addinin Allah, da kuma kare lafiyar Manzon Allah (saww) fiye da komai.

Sun bama Allah kyautar dukiyoyinsu da basirorinsu da Qarfinsu, karshe ma har rayukansu suke rige-rigen bayarwa domin Allah da Manzonsa (saww).

Ya Allah ka saka musu da alkhairi, ka Qara yardarka garesu, ka bamu albarkarsu, ka riskar damu zuwa garesu cikin aminci. Kada ka karbi rayukanmu har sai mun samu yardarka cikin falalarka da rahamarka Ya Mafi Karamci da Girman daraja! Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/10/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI