MU SAN ANNABINMU (SAWW) - 1
NASABARSA :
**************
Shine Shugabanmu Muhammadu 'dan Abdullahi 'dan Abdul Muttalibi 'dan Hashim 'dan Abdu Manafi 'dan Qusayyu 'dan Kilabu 'dan Murratu 'dan Ka'abu 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu 'dan Fihru 'dan Maliku 'dan Nadhru 'dan Kinanatu 'dan Khuzaimah 'dan Mudrikah 'dan Ilyas 'dan Mudhar 'dan Nizaar 'dan Ma'addu 'dan 'Adnan shi kuma Adnan yana daga cikin jikokin Annabi Isma'il (as) shi kuma 'dan Annabi Ibraheem (as).
Nasabah ce tsarkakakkiya wacce babu wani datti ko Qazanta irin ta zamanin jahiliyyah da ta ta'ba ratsata. Kowanne daga cikin iyayensa da kakanninsa tsarkakakke ne kuma mafi nagartar mutanen zamaninsa. Haka kuma iyayensa mata dukkaninsu tsarkaka ne madaukaka acikin jama'ar zamunnansu.
Shi da kansa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "NI ZA'BABBE NE DAGA CIKIN ZABABBU DAGA CIKIN ZABABBU".
Allah ya zabi zuriyar gidan Annabi Isma'il (as) daga cikin halittu, Kuma ya zabi Qabilar larabawa daga cikin 'ya'yan Isma'eel (as) kuma ya za'bi Qabilar Quraishawa daga cikin larabawa, kuma ya za'bi Banu Kinanah daga cikin Quraishawa, kuma ya za'bi Banu Hashim daga cikin banu Kinanah, sannan ya za'bi Annabinmu (saww) daga cikin banu Hashim.
Salatin Allah da amincinsa mafi girma mafi tsarki mafi yawa, mafi yalwa, mafi wanzuwa su tabbata bisa Shugaban Shugabanni Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da Sahabbansa tare da dukkan masu binsu daga kyautatawa har zuwa ranar Mahshar.
Comments
Post a Comment