Posts

YA KAI MAI NEMAN KUSANCI

Idan kaga mutane sun nuna wadatuwarsu da duniya, kai kuma sai ka wadatu da Allah. Idan kuma kaga suna nuna farin cikinsu da duniya, To kai kuma kayi farin ciki da Allah. Idan kaga mutane suna debe kewarsu da duniya, kai kuma ka sanya debe kewarka (wato samun nutsuwarka) da Allah. Idan kaga mutane suna neman shiga wajen Sarakunansu da manyansu, suna neman kusanci dasu domin su samu Girma da daukaka, to kai kuma ka nemi kusanci da Allah da kuma Soyayyarsa ta wannan hanyar zaka samu Mutukar girma da daukaka. NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990) - (31-01-2017).

YA SAKETA ACIKIN IDDAH

YA QARA SAKINTA ACIKIN IDDAH TA MBAYA TA 2025 ******************* Aslkm Wa rahmatullahi Wa barakatuhu. Don Allah zauren Fiqhu, Ina son a kara warware min wannan matsalan. Mijina ne ya ce nasakeki saki daya, toh ina cikin wancan iddah ban kare ba sai yace ya kara daya. Shine nake son inji sakin na biyun yayi ko baiyi ba?. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Eh lallai ya halatta ga Mijinki ya Qara yin wani sakin bayan wannan na farkon da yayi, koda kina cikin iddah. Kuma sakin ya yiwu. Da ache kin riga kin Qare iddar farko ne, to kin fita daga hannunsa baki daya. Bashi da wannan damar. Amma ayanzu kam wannan sakin ya yiwu. Idan kika kammala jininki uku shikenan kina da damar kije ki auri wani sabon Mijin. Allah ya sawwake, Allah ya daidaita tsakanin dukkan Ma'auratan da suke cikin rikici. WALLAHU A'ALAM. D AG A ZAUREN FIQHU 14-11-2016 (14-02-1438).

MAGANIN CIWON TSAKUWAR UWAR HANJI

TAMBAYA TA 2021 ******************** Assalamu alaikum Zauren Fiqhu, fatan alkhairi da godiya ga Malam. Ni dalibi ne a wannan zaure mai albarka na shafin facebook, Ina fama da wani irin ciwon ciki ne wanda idan ya rike ni ko tashi tsaye inyi tafiya mai kyau bana iyawa, kuma nayi scanning har sau uku amma ba komai take nunawa ba, sai yau danayi awani asibitin sukayi confirming appendixes ne. Don  Allah Malam ban Sani ba ko akwai wasu magungunan da zan iya amfani dasu Wanda ba sai anyimin operation ba. JAZAKUMALLAH BI AHSANUL KHAIR. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko dai muna yi maka fatan alkhairi da fatan Allah ya baka lafiya daga dukkan abinda ke damunka. Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon in sha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata anan Zauren Fiqhu. Ga wasu nan kamar haka : 1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa coka...

BANKUNAN AJIYAR RUWAN MANIYYI

Yanzun nan ina zaune sai naga shigowar wata wasika daga wani 'Dan uwa kuma member a Zauren Fiqhu Whatsapp -1. Yana jan hankalina zuwa ga karanta wani bayani da ya kwafo ya turo mun. (Daga shafin wata Jaridar Qasar nan). Wato bayanin yana kunshe ne da wani Quduri wanda wata Cibiyar binciken yanayin rayuwa da kuma tattalin arzikin Nigeria (NISER) dake Ibadan ta gabatar. Cibiyar tayi kira ne ga Gwamnatin Tarayyar Nigeria cewar ta kafa "SPERM BANKS" (Rumbunan ajiyar ruwan Maniyyi da Qoyayyen Halitta) a sasannin Nigeria. Cibiyar ta gabatar da wannan kiran ne acikin wata takarda wacce daya daga cikin Wakilanta DR THERESA ORIAKU EMORDI ta Jami'ar Obafemi Awolowa ta gabatar awajen wata Seminar. Sun bukaci ma asanya Qudurin ya zama doka a Qasar nan cewa Matsalar rashin haihuwa dole sai an magance matsalar rashin haihuwa atsakanin Ma'aurata. Shi dai wannan bankin ajiyar Maniyyi idan har an Qirkireshi, to zai bada damar kowanne m...

HUKUNCIN AMSA SALLAMAR WANDA BA MUSULMI BA

TAMBAYA TA 2001 ******************** Assalamu alaikum. Allah ya qarawa malam Eamani ya jiqan iyaye. Ameen, tambaya nake roqon a amsa min. Yaya hukuncin Wanda ya shaaku da Wanda ba musulmi ba kuma ya dauke shi a matsayin aboki? kuma shin ya kamata a mayar ma Wanda ba musulmi sallama  idan yace ma Assalamu alaikum?. Dafatan malam zai samu damar amsa tambayata. daga dalibinka Ibraheem I g AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Allah Madaukakin Sarki ya umurcemu da cewa kada mu riki Yahudu da Nasaara amatsayin Masoya ko Majibinta garemu. Ba don komai ba, sai domin sharrin da irin hakan zai haifar ga rayuwarmu da addininmu. Allah Madaukakin Sarki yace : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI! KADA KU RIKI YAHUDU DA NASAARA AMATSAYIN MAJIBINTA (WATO ABOKAI KO MASOYA) SASHENSU MAJIBINTA NE GA SASHE. DUK WANDA YA JIBINCESU DAGA CIKINKU TO HAKIKA SHIMA YANA CIKINSU. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRIYAR DA MUTANE AZZALUMAI". (Ma'idah ayah ta 51). Ibnu Abi Hatam ya ...

ANNABI MASOYIN AL'UMMARSA (SAWW).

``` Hakika in dai zamuyi adalci, to tabbas babu wanda ya kamata muso shi, Mu bishi, mu girmamashi, Mu kambama shi, Kamar Manzon Allah (saww). Shi ya kamata Muyi soyayya don soyayyarsa, Muyi kiyayya don kiyayyarsa kamar yadda Allah yake yi. Domin babu wanda yasomu, ya damu da sha'aninmu, Kuma yake tausayinmu Kamar Annabi Muhammadu (saww). Zan kawo wasu Misalai daga cikin irin soyayyarsa da kulawarsa garemu kamar haka : 1. Lokacin da Kafirai suka matsa wajen chutar dashi da mabiyansa, an nemi alfarma agareshi cewa ko zai yi addu'a irin wacce Annabi Nouhu (as) yayi, sai yace "A'a. Ya Allah ka shiryi Mutanena. Domin su basu sanni bane". Kunga da ache yayi waccan addu'ar, da tuntuni mun hallaka. To amma da yake shi BIL MU'UMINEENA RA'UUFUN RAHEEMUN ne, sai bai yi haka ba. Yayi mana alkhairin da babu iyaka. 2. Lokacin fitar rai, kowa ya san cewar mutum ba ya iya tunawa da kowa awannan lokacin. Ta kansa yakeyi. Amma Manzon Allah (saww) bai manta damu ba....