Posts

Showing posts from January, 2018

ALLAH YAFI GABAN KWATANCE

Hakika Allah Madaukakin Sarki, Samamme ne tun gabannin samuwa. Kuma dawwamamme ne ba tare da farko ko Qarshe ba. Babu Jihar da take ritsashi, kuma babu wajen da ake rasashi. Shi Makadaici ne wanda Qirge ko lissafi basu riskarsa. Yafi gaban kwatance da zuciya ko tunanin masu tunani. Bai haifa ba, kuma ba'a haifeshi ba. Shine abin nufin dukkan halittu. Kuma babu wani kini agareshi. Bai yi kama da komai ba, kuma babu abinda yayi kama dashi. Shi Mawadaci ne ba ya bukatar komai awajen kowa, shine wanda kowa ke bukatar komai awajensa. Mai cikakken iko ne wanda ikonsa bai rataya da zamani ko makani ba. Kuma mai nufi ne ga dukkan abinda yaso. Babu mai tambayarsa akan abinda yayi, kuma babu mai tuhumarsa akan abinda bai so kasantuwarsa ba. Shi Masani ne tun gabannin komai. Shi yasan komai, kuma ya san kowa. Amma babu wanda ya sanshi sai shi kansa. Shi Rayayye ne tun gabannin dukkan rayayyu. Kuma shi rayayyen bayan macewar dukkan rayayyu. Rayuwarsa bata ratayu da komai ba. Kuma bata do

MAI DA'DIN SUNAYE SAWW (06)

Amincin Allah ya tabbata agareku 'Yan uwana cikin So da girmamawa ga Annabin Rahama (saww). Wannan itace fitowa ta shida (6) cikin darasin Zauren Fiqhu mai taken "Mai da'din sunaye" . Wanda acikinsa suke yin sharhi tare da bayanai game da sunayen Manzon Allah (saww) kuma mafiya yawan bayanan muna cirosu ne daga cikin litattafan manyan Maluman wannan al'ummah. Musamman "Zadul Ma'ad" na Ibnu Qayyimil Jauziyyah. Mun tsaya kan suna na takwas, yanzu kuma in shaAllah zamu ci gaba daga nan : 9. NABIYYUL MULHIMAH : Wato "ANNABI SHA-GWAGWARMAYA". Ma'anarsa shine Annabin da Allah ya aikoshi da Yaqi da Maqiyan Allah. Domin hakika babu wani Annabin da yayi yaqi tare da magoya bayansa daga al'ummarsa kamar irin yadda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Kuma irin Yaqe-yaqen da suka afku tsakanin al'ummarsa da kuma kafirai, Yaqe-yaqe ne wadanda ba'a ta'ba ganin irinsu ba acikin tarihin duniya. Domin al'umma

LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA!!!

Abdullahi bn Almubarak (rah) yana daga cikin magabata na kwarai, kuma mutum ne Salihi. Wata shekara bayan yayi niyyar tafiya aikin Hajji, sai ya fita domin yin ban-kwana da abokansa (Almajiransa) kafin tafiyarsa. Amma akan hanyar ne yaga wani abu wanda ya tada masa hankali ya firgitashi. Ya hangi wata baiwar Allah tana tone juji (bola) tana tonowa wani MUSHEN KAZA wacce aka jefar. Ta daukota ta sanya a Qasan hammatarta, ta juya ta tafi aboye acikin duhu. Sai yayi kiranta yace "Mai kikieyi ya ke baiwar Allah?!". Sai tace "Ya kai bawan Allah,  kyale halittu da mahaliccinsu. Domin Allah yana da sha'ani acikin lamarin halittunsa". Sai Ibnul Mubarak yace mata "Ina yi miki magiya don girman Allah ki gaya min labarinki". Sai matar tace masa "Amma wallahi ba don ka riga kayi mun magiya ba, da ban gaya maka halin da nake ciki ba". Kafin ta fara gaya masa har hawaye ya fara zuba daga idanunta. Sai tace "Hakika mu Allah ya halatta mana cin

BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (SAWW) - 5

BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (05) *********************************** Yana daga cikin Mu'ujizozin Annabinmu Muhammadu (saww) da kuma alamomin Manzancinsa cewa Allah ya hore masa dukkan halittu masu motsi da marassa motsi sunyi imani dashi, sun shaidar da Manzancinsa kuma suna yin biyayya gareshi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam). Wannan shine kashi na biyar cikin bayanin irin wadannan Mu'ujizozin : Hadeethi daga Sayyiduna Ya'ala bn Murrah Ath-Thaqafiy (rta) acikin wani dogon hadithi yace : "Sai muka ci gaba da tafiya tare da Manzon Allah (saww) har sai da muka sauka awani masauki sai Manzon Allah (saww) yayi barci. Sai ga wata bishiya ta taho tana Tsaga Qasa har sai da ta lullubeshi sannan ta koma wajen da take. Yayin da Manzon Allah (saww) ya farka na ambata masa abinda ya faru sai yace : "ITA DIN WATA BISHIYA CE WACCE TA NEMI IZININ UBANGIJINTA CEWA ZATA GAISHENI.. KUMA YAYI MATA IZINI". Imamul Bagawiy ne ya ruwaito hadisin acikin Sharhus Sun

IDANUWAN MANZON ALLAH (SAWW)

Wadannan idanuwa na Manzon Allah (saww), idanuwa ne wadanda darajarsu tafi duniya da lahira da abinda ke cikinsu. Kai har alahirar ma babu abinda ya fisu daraja. Idanuwa ne wadanda basu ta'ba sa'ba ma Allah ba. Allah ya tsarkakesu ya girmamasu,  Har ma yana yabonsu acikin Alqur'ani mai girma yana cewa: "MA ZAAGHAL-BASARU WAMA TAGHAA ". Idanuwa ne wadanda suka kalli abinda wani ido bai ta'ba gani ba. Allah Madaukakin Sarki ya shaidar da haka inda yake cewa : " LAQAD RO'AA MIN AAYATI ROBBIHIL KUBRAA ". " HAKIKA YA GANI DAGA MANYAN AYOYIN UBANGIJINSA ". Kuma akwai hadisai da dama wadanda acikinsu Manzon Allah (saww) yake bamu labarin wasu daga cikin abubuwan da ya gani da wannan idanuwan, wadanda babu wani mahalukin da ya ta'ba gani in banda SHI (SAWW). SIFFAR IDANUNSA DA GASHIN GIRARSA ( SAWW ) : MASU SIFFANTA SHI (SAWW) irinsu Ameerul-Mu'umineen Sayyiduna Aliy bn Aby Talib, Sayyiduna Abu Huraira, Sayyiduna Hi

MADUBIN DUBAWA (32)

Watarana Muhammad bn Ziyad (rah) ya tambayi Ibraheemul Khawwas (rah) cewa "Tunda kake yawo cikin dazuzzuka wanne abu ka ta'ba gani wanda yafi baka mamaki?". Sai yace "Na kasance watarana acikin dokar daji, Sai na kwanta nayi barci akan wani dutse. Sai ga wani Shaitanin Aljani yazo ya tsaya akaina yace mun "Ka tashi daga nan". Sai nace masa "Tafi ka ban waje.Ba zan tashi ba". Sai yace mun "Zan Takeka da Qafata, Kuma zaka hallaka". Sai nace masa "Yi duk abinda kaga dama". Yayin da ya takani, (Ban ji komai ba) Qafar tasa kamar nauyi fallen takarda take. Sai Shaitanin yace mun "Amma lallai kai Waliyyin Allah ne. Don Allah yaya sunanka?". Sai nace masa "Nine Ibrahimul Khawwas". 'Yan uwa wannan yana nuna mana irin tasirin da addu'a take dashi akan Shaitanun Aljanu. Kuma yana nuna mana irin yadda shaitanu sukayi nisa wajen shuka sharri, tunda gashi har suna iya yin yunkurin chutar da Manyan bayin

YAFI TURARE QAMSHI (SAWW)

Ummu 'Aasim ( ra ) matar Sayyiduna 'Utbatu bn Farqad ( ra ) ta bada wani  labari mai ban-mamaki tana cewa: " Mu hudu ne Matayen dake auren 'Utbah ( ra ) kuma mun kasance kowacce daga cikinmu tana gasar shafa turare mafi Qamshi fiye da abokiyar zamanta , amma duk da haka shi Mijin namu ( Utbah ) ya fimu Qamshin jiki , alhali kuma bamu ta'ba ganinsa ya shafa turare ba . Sai dai ya shafa ma gemunsa mai. Mijin namu ya kasance idan ya shiga cikin mutane sai kaji suna cewa "Kai! Bamu ta'ba jin turare mai Qamshi kamar na Utbatu ba ". Watarana sai nace masa " Mu ( Matanka ) mun kasance muna gasar sayen turare mafiya Qamshi amma duk da haka kai kafi mu Qamshin jiki . Wai menene dalili ?". Sai yace " Warin jiki ne ya dameni azamanin Manzon Allah ( saww ) sai naje na gaya masa . Sai ya umurceni in tube rigar dake jikina , sai na tube na zauna