IDANUWAN MANZON ALLAH (SAWW)
Wadannan idanuwa na Manzon Allah (saww), idanuwa ne wadanda darajarsu tafi duniya da lahira da abinda ke cikinsu. Kai har alahirar ma babu abinda ya fisu daraja.
Idanuwa ne wadanda basu ta'ba sa'ba ma Allah ba. Allah ya tsarkakesu ya girmamasu, Har ma yana yabonsu acikin Alqur'ani mai girma yana cewa:
"MA ZAAGHAL-BASARU WAMA TAGHAA".
Idanuwa ne wadanda suka kalli abinda wani ido bai ta'ba gani ba. Allah Madaukakin Sarki ya shaidar da haka inda yake cewa :
"LAQAD RO'AA MIN AAYATI ROBBIHIL KUBRAA".
"HAKIKA YA GANI DAGA MANYAN AYOYIN UBANGIJINSA".
Kuma akwai hadisai da dama wadanda acikinsu Manzon Allah (saww) yake bamu labarin wasu daga cikin abubuwan da ya gani da wannan idanuwan, wadanda babu wani mahalukin da ya ta'ba gani in banda SHI (SAWW).
SIFFAR IDANUNSA DA GASHIN GIRARSA(SAWW) :
MASU SIFFANTA SHI (SAWW) irinsu Ameerul-Mu'umineen Sayyiduna Aliy bn Aby Talib, Sayyiduna Abu Huraira, Sayyiduna Hind bn Aby Haala, Sayyidah Ummu Ma'abad Al-Khuza'iyyah (Allah ya kara musu yarda) Sunce:
"MANZON ALLAH (saww) yana da Mayalwatan Idanuwa masu tsananin kyawu. Wajen Farin, Fari Qal yake. Hakanan Qwayar idanunsa baki-Qirin take.
Sannan akwai ratsin-Jaa acikin kwayar idanun. Wanda hakan yana daga alamomin cikar Annabtarsa kamar yadda Annabawan Farko suka gayawa al'ummominsu.
Hafiz Al-Iraaqee ya ruwaito cewa Lokacin da Manzon Allah (saww) Ya hadu da Raahib dinnan alokacin da suka je fatauci tare da Maisara (bawan Nana Khadeeja ra) acikin garin Basra, Farkon shaidar da Raahib din ya fara dubawa ajikin Manzon Allah (saww) ita ce Wannan RATSIN JA na cikin idanunsa.
Daga gani sai ya tabbatar cewa WANNAN SHINE ANNABIN QARSHE (SAWW).
(aduba Sharhin Shama'il na Imamul-Manawy juzu'i na 1, shafi na 55).
Sannan yana da Mayalwacin gashin idanu. Gashin baqi ne, ko yaushe haka zaka ganshi kamar yasa tozali.
Na saman ya Tankwara izuwa sama, sannan na kasan shi kuwa ya tintsira Izuwa Qasa.
Yana da cikakken Gashin girarsa mai kyawu ga Tsawo, kuma ya lankwashe kamar baka.
Saboda kwarjininsa da kyawunsa Zaka ga girarsa ta dama data haggu kamar sun hade, amma basu hadu ba. Karan Hancinsa ya dan raba tsakaninsu.
(haka Ibnul Atheer ya fada acikin Nihaya, da kuma Sheikh Yusufun-Nabahany acikin Wasa'ilul-Wusul, Shafi na 73, da kuma Mulla Aliyul-Qary acikin JAM'UL-WASA'IL Juzu'i na 1 shafi na 44.).
YA ALLAH KA QARA MANA SOYAYYAR NAJAMUL-HUDA (SAWW).
Idan an ta'ba Allah yakan yi fushi (saww) sai kaga wata jijiya ta fito atsakanin girarsa (saww).
TOZALINSA MAI ALBARKA (SAWW)
************************************
Sanya tozali yana daga cikin Sunnoninsa (saww). Domin ko sanda aka haife shi (saww), yazo Idanunsa radau da tozali.
Sayyiduna Abdullahi bn Abbas ya ruwaito cewar Manzon Allah (saww) ya kasance yana shafa tozalin Ithmud acikin Idanunsa kullum da daddare kafin ya kwanta, Sau Uku a idon dama sannan sau uku a idon haggu.
Har ma yana cewa "Kuyi tozali da Ithmud. Domin yana Qara Qarfin idanu, kuma yana tsirar da gashi".
(aduba Sunanut-Tirmidhy, Hadisi na 1757, da Kuma Mustadrak na Imamul-Hakim Hadisi na 8249).
QARFIN IDANUNSA (SAWW)
****************************
MANZON ALLAH (AS) Ya kasance yana gani acikin duhu kamar yadda yake gani acikin haske. Sannan yana ganin abinda ke nesa kamar yadda yake ganin na Kusa.
Idan ya kalli gabas yana iya ganin Mahudar rana, hakanan idan ya kalli yamma yana iya ganin mafadar rana.Kuma Yana iya shaida matafiyin dake nesa tun kafin afara ganin Qurarsa.
An ruwaito cewar Manzon Allah (saww) yana iya Qirga taurari 11 acikin Taurarin nan mafiya nisa na Surayyah.
Mala'ika Jibreelu yakan nado masa Doron Qasar nan gaba dayanta ya, ajiye masa agabansa ya kalli kowanne sashe.
In banda SHI (SAWW) babu wani Annabin da ya ta'ba ganin Mala'ika JIBREELU (AS) abisa Surar da Allah ya halicce shi da ita. Kuma da wannan idanuwan ya kalleshi.
Wannan Idanun nasa masu albarka, dasu ne yaje yaga Aljannah da ni'imomin da suke cikinta, Sannan yaga wuta da Ukubobin da suke cikinta.
Wadannan idanun na Manzon Allah (saww) dasu ne yayi kallo izuwa AJA'IBU (ABUBUWAN MAMAKI) NA MALAKUTUN UBANGIJINSA acikin daren da akayi Isra'i da Mi'iraji dashi (saww).
Yaga dukkan Annabawan Allah (as). Yaga Al'arshu da Kursiyyu da Lauhu da Qalamu da Haudhu da Raf-rafu. Kuma yaga Kogunan haske, Sannan ya ratsa Miliyoyin hijabai duk da wannan idanun.
Yaga Baitul-Ma'amur yaga Mala'iku nau'i-nau'i. Yaga Raf-Rafu da Farshu, har sanda yaga UBANGIJINSA (SWT) alokacin da sukayi Munajati awajen da Ubangijin nasa yaso.
Akwai sa'bani atsakanin Malaman Farko har zuwa yanzu game da maganar Shin Annabi (saww) yaga Allah ne ko bai ganshi ba?.
Nana A'ishah (ra) tace bai ganshi ba. Amma Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (Malamin al'ummah) yayin da aka tambayeshi yace : "YA GANSHI! YA GANSHI! YA GANSHI! YA GANSHI! (Yayi ta maimaitawa har sai da ya shiɗe).
Anan zan Tsaya sai mun hadu acikin wani darasin da zamu gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp in sha Allah.
YA Allah kara salati da sallama marasa iyaka abisa Zababben Zababbu (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (Asalin rubutun na yishi ne aranar 09/APRIL/2013).
Comments
Post a Comment