YAFI TURARE QAMSHI (SAWW)

Ummu 'Aasim (ra) matar Sayyiduna 'Utbatu bn Farqad (ra) ta bada wani  labari mai ban-mamaki tana cewa:

"Mu hudu ne Matayen dake auren 'Utbah (ra) kuma mun kasance kowacce daga cikinmu tana gasar shafa turare mafi Qamshi fiye da abokiyar zamanta, amma duk da haka shi Mijin namu (Utbah) ya fimu Qamshin jiki, alhali kuma bamu ta'ba ganinsa ya shafa turare ba. Sai dai ya shafa ma gemunsa mai.

Mijin namu ya kasance idan ya shiga cikin mutane sai kaji suna cewa "Kai! Bamu ta'ba jin turare mai Qamshi kamar na Utbatu ba".

Watarana sai nace masa "Mu (Matanka) mun kasance muna gasar sayen turare mafiya Qamshi amma duk da haka kai kafi mu Qamshin jiki. Wai menene dalili?".

Sai yace "Warin jiki ne ya dameni azamanin Manzon Allah (saww) sai naje na gaya masa. Sai ya umurceni in tube rigar dake jikina, sai na tube na zauna agabansa, na dora rigata agabana.

Sai Manzon Allah (saww) yayi tofi a tafin hannunsa mai albarka sannan ya shafi cikina da Qirjina da hannunsa. Tun daga ranan ne sai wannan Qamshin yake fitowa ta jikina".

(Imam Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).

Salati da aminci su tabbata agareka Ya RASULALLAHI adadin yardar Ubangiji da Yalwar kalmominsa da dawwamar Mulkinsa da tsarkin zatinsa. Albarkacin wannan Salatin Ya Allah ka azurtamu da jin Qamshin jikinsa tun muna raye, da ranar mutuwarmu, da ranar tashinmu. Kuma ka azurtamu da samun Makwabtaka dashi ta har abada acikin Aljannarka Firdausi. Aameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU 04-04-1438 (03-01-2017)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI