MAI DA'DIN SUNAYE SAWW (06)


Amincin Allah ya tabbata agareku 'Yan uwana cikin So da girmamawa ga Annabin Rahama (saww). Wannan itace fitowa ta shida (6) cikin darasin Zauren Fiqhu mai taken "Mai da'din sunaye" . Wanda acikinsa suke yin sharhi tare da bayanai game da sunayen Manzon Allah (saww) kuma mafiya yawan bayanan muna cirosu ne daga cikin litattafan manyan Maluman wannan al'ummah. Musamman "Zadul Ma'ad" na Ibnu Qayyimil Jauziyyah.

Mun tsaya kan suna na takwas, yanzu kuma in shaAllah zamu ci gaba daga nan :

9. NABIYYUL MULHIMAH : Wato "ANNABI SHA-GWAGWARMAYA". Ma'anarsa shine Annabin da Allah ya aikoshi da Yaqi da Maqiyan Allah. Domin hakika babu wani Annabin da yayi yaqi tare da magoya bayansa daga al'ummarsa kamar irin yadda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Kuma irin Yaqe-yaqen da suka afku tsakanin al'ummarsa da kuma kafirai, Yaqe-yaqe ne wadanda ba'a ta'ba ganin irinsu ba acikin tarihin duniya.

Domin al'ummarsa su suke Qille kan kafirai su karkashesu akowanne lungu da saqo abayan qasa, kuma acikin zamunna masu bibiyar juna.

Ku dubi dai faman da akayi aranar Badar da Uhudu da Khaybara da Hunainu.. Ku binciki mai ya faru aranar Yaqin Gwalalo (Khandaq), da Hamra'ul Asad da Zatur Riqa'i da ranar Banul Mustalaq, da kuma wahalar da aka sha lokacin tafiya Tabuka da dawowa..

Sannan ku dubi yadda Sahabbansa suka sha fama ranar Yaqin Mu'utah, da Bi'iru Ma'unah, da sauran Yaqe-yaqen da suka faru azamaninsa.. Har dai daga Qarshe ya samu gagarumar nasarar bude garinsa na Makkah.. Ranar da tarihi bai ta'ba ganin tamkarta ba.

Lallai koda abayansa haka Sahabbansa suka sha fama da dakarun daulolin kafirci na Farisa da Ruma da sauransu. Har dai daga karshe addinin Allah ya samu ya'duwa tare da cikakkiyar kariya ga mabiyansa.  Alhamdulillah.

10. NABIYYUR RAHMATI (SAWW) : Shine Annabin Rahama, Annabin da Allah ya aikoshi domin cikar rahamarsa ga dukkan talikai baki daya.

Dashi ne Allah yayi rahama ga dukkan halittun dake doron Qasa baki daya, kafiransu da muminansu. Aljanunsu da mutanensu har ma da Mala'iku. Da dabbobi da tsuntsaye.. Har ma abubuwan da basu motsi  duk wannan rahamar ta gamesu baki daya.

Amma muminai sune suka samu rabo mafi girma daga wannan rahamar. Su kuwa kafirai da Ahlul Kitabi sun zauna Qarkashin inuwarsa da Alqawarin samun kariyarsa.. Wadanda kuma Sahabbansa suka kashe daga cikin kafirai, to sun gaggauta turasu ne zuwa mummunar makomar dake jiransu (Wato Wuta). Kuma sun hutar dashi kafirin kenan daga tsawon rayuwar da ba zata Qara masa komai ba in banda tsananin azabar lahira.

Hakika dukkan sunayensa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) haka suke cike da ma'anoni da fassarori na fili da boye. Sai dai muyi fatan Allah ya buda idanuwan basirorinmu yadda zamu fahimta kuma mu amfana da abinda ke Qunshe cikinsu. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (23/01/2018 05/05/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI