BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (SAWW) - 5

BIYAYYAR BISHIYOYI GARESHI (05)
***********************************
Yana daga cikin Mu'ujizozin Annabinmu Muhammadu (saww) da kuma alamomin Manzancinsa cewa Allah ya hore masa dukkan halittu masu motsi da marassa motsi sunyi imani dashi, sun shaidar da Manzancinsa kuma suna yin biyayya gareshi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Wannan shine kashi na biyar cikin bayanin irin wadannan Mu'ujizozin :

Hadeethi daga Sayyiduna Ya'ala bn Murrah Ath-Thaqafiy (rta) acikin wani dogon hadithi yace :

"Sai muka ci gaba da tafiya tare da Manzon Allah (saww) har sai da muka sauka awani masauki sai Manzon Allah (saww) yayi barci.

Sai ga wata bishiya ta taho tana Tsaga Qasa har sai da ta lullubeshi sannan ta koma wajen da take.

Yayin da Manzon Allah (saww) ya farka na ambata masa abinda ya faru sai yace :

"ITA DIN WATA BISHIYA CE WACCE TA NEMI IZININ UBANGIJINTA CEWA ZATA GAISHENI.. KUMA YAYI MATA IZINI".

Imamul Bagawiy ne ya ruwaito hadisin acikin Sharhus Sunnah.

Muma Allah ya umurcemu muyi Salati da gaisuwa agareshi :

Assalamu alaika Ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Assalamu alaika Ayyuhan Nabiyyul Arabiyyul Hashimiyyu.

Assalamu alaika Ayyuhash Shafi'ul Mushaffa'i yaumal Qiyamah.

Assalamu alaika Ya Ãqibun Muqaffan Li Jamee'il Anbiya'i War Rusuli.

Assalamu alaika Ya Sahibal Maqamil Mahmudi.

Assalamu alaika Ya Sahibal Liwa'il Hamdi.

Assalamu alaika Ya Qa'idal Ghurril Muhajjaleen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (20/04/1439  08/01/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI