MADUBIN DUBAWA (32)
Watarana Muhammad bn Ziyad (rah) ya tambayi Ibraheemul Khawwas (rah) cewa "Tunda kake yawo cikin dazuzzuka wanne abu ka ta'ba gani wanda yafi baka mamaki?".
Sai yace "Na kasance watarana acikin dokar daji, Sai na kwanta nayi barci akan wani dutse.
Sai ga wani Shaitanin Aljani yazo ya tsaya akaina yace mun "Ka tashi daga nan".
Sai nace masa "Tafi ka ban waje.Ba zan tashi ba".
Sai yace mun "Zan Takeka da Qafata, Kuma zaka hallaka".
Sai nace masa "Yi duk abinda kaga dama".
Yayin da ya takani, (Ban ji komai ba) Qafar tasa kamar nauyi fallen takarda take.
Sai Shaitanin yace mun "Amma lallai kai Waliyyin Allah ne. Don Allah yaya sunanka?".
Sai nace masa "Nine Ibrahimul Khawwas".
'Yan uwa wannan yana nuna mana irin tasirin da addu'a take dashi akan Shaitanun Aljanu. Kuma yana nuna mana irin yadda shaitanu sukayi nisa wajen shuka sharri, tunda gashi har suna iya yin yunkurin chutar da Manyan bayin Allah irin su Ibraheemul Khawwas (rah).
Allah shi Qara mana himma da kwazo wajen rike addu'o'in neman kariya daga sharrin Shaitanun dare da rana. Aameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU 06-04-1438 (04-01-2017)
Comments
Post a Comment