MADUBIN DUBAWA (75)
QARSHEN MAI CI DA ADDINI ***************************** Al Imam Ibnul Jauzee ya hakaito daga Uthman bn Abdillah cewa a zamanin Annabi Musa (amincin Allah ya tabbata gareshi da Annabinmu) akwai wani mutum wanda yake hidimta masa, kuma yana neman ilimi awajensa. Watarana sai wannan mutumin ya nemi izini awajen Annabi Musa (alaihis salam) cewa yana so zai je garinsu ya dawo. Sai Annabi Musa (alaihis salam) yayi masa izini ya tafi. Amma daga zuwansa sai ya mayar da kansa tamkar shine malamin garin. Yana tashi yana wa'azi atsakanin mutanen garin, motsi ka'dan sai yace musu "Musa kaleemul Lahi (alaihis salam) ya bani labari cewa kaza yayi kaza". Ko kuma "Annabi Musa mai ganawa da Allah ya bani labari cewa kaza yayi kaza... ". Su kuma mutanen garin suna jin dadi suna tara masa dukiya har dai ya tara kudi da dukiya mai yawan gaske. Kuma daga nan ya zauna agarinsu bai sake komawa wajen Annabi Musan ba. Shi kuwa Annabi Musa (alaihis salam) ya kasance yana yawan t